Kotu ta yi watsi da karar masu nadin Sarki a Kano

Alkalin babbar kotun Ahmad Badamasi ya ce abubuwa da dama sun sha gaban karar.

Asalin hoton, MUHD KANO EMIRATE PHOTOGRAPHY

Wata babbar kotu a Kano da ke arewacin Najeriya ta yi fatali da karar da masu nadin Sarki a jihar suka shigar domin kalubalantar gwamnatin jihar kan kirkiro sabbin masarautu.

A shekarar 2019 ne Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya kirkiro da sabbin masarautun yanka hudu da kuma nadin sarakuna masu daraja ta daya a jihar.

Masarautun su ne Gaya da Rano da Bichi da kuma Karaye. Hakan ya sa ana da masarautun yanka biyar ke nan a jihar, baya ga ta kwaryar birnin Kano, wacce Sarki Muhammadu Sanusi II yake jagoranta.

Lamarin dai bai yi wa masu nada sarki a Kano dadi ba, abin da ya sa suka shigar da gwamnati kara a kotu.

Sai dai da yake yanke hukunci a ranar Litinin, alkali Ahmad Badamasi na babbar kotun ya ce abubuwa da dama sun sha gaban karar yayin da hukuncin da alkali Usman Na'abba ya yanke ranar 21 ga watan Nuwamba ya soke dokar da ta kirkiri sabbin masarautun.

Masu nadin sarkin hudu da suka shigar da karar su ne Hakimin Dawakin Tofa Yusuf Nabahani (Madakin Kano) da Hakimin Wudil Abdullahi Sarki Ibrahim (Makaman Kano) da Hakimin Gabasawa Bello Abubakar (Sarkin Dawaki Mai Tuta da Hakimin Dambatta Mukhtar Adnan (Sarkin Ban Kano).

Premium Times ta rawaito cewa dukkan masu nadin sarkin hudu sun rasa mukaminsu na Hakimi sannan an nada wadanda za su maye gurbinsu.

Wadanda ake kara su ne gwamnatin Kano da gwamnan jihar da shugaban majalisar dokokin Kano da majalisar dokokin jihar da alkalin alkalai na jihar.

Kazalika akwai sabbin sarakunan Aminu Ado Bayero Sarkin Bichi da Ibrahim Abubakar Sarkin Karaye da Tafida Abubakar Sarkin Rano da Ibrahim Abdulkadir Sarkin Gaya.