Shin kiran Shugaba Buhari na a daina yin ramuwar gayya zai yi tasiri?

An kashe akala mutum 30 a harin da aka kai a kauyukan Katsina makon jiya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An kashe akala mutum 30 a harin da aka kai a kauyukan Katsina makon jiya

Masana harkokin tsaro a Najeriya sun ce abu ne mai wahala 'yan kasar su saurari kiran da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kan su daina hukunta masu satar mutane ko 'yan fashin daji da kansu.

Wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar ce ta yi kira ga 'yan Najeriya su daina kashe ko dukan wadanda aka kama da laifin kai hare-hare, tana mai kira da su rka mika su ga hukumomin tsaro.

Kiran na zuwa ne bayan hare-haren ramuwar gayya da wasu 'yan bindiga suka kai wa wasu kauyukan karamar hukumar Batsari a jihar Katsina a makon jiya inda aka kashe akalla mutum talatin.

Shugaba Buhari ya yi kiran ne a wata sanarwar jaje kan hare-haren, wadda kakakinsa Garba Shehu ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Ya ce kashe mutane domin ramuwar gayya bai dace ba kuma babu wanda ke da ikon yin gaban kansa wajen hukunta mai laifi.

Amma wani mai sharhi kan lamuran tsaro a Najeriya, Dakta Kabiru Adamu, ya ce ba ya jin kiran shugaban zai yi tasiri sosai saboda 'yan Najeriya na ganin jami'an tsaro suna gaza aiwatar da ayyukansu.

Ya ce: "Kira ne mai kyau kuma da ma duk wani shugaba ya kamata ya yi irin wannan kiran; amma matsalar ita ce dole ne ke sa mazauna kauyuka a Najeriya daukar matakin tsaro a hannunsu."

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

"A kauyuka da yawa idan aka kama masu laifi jami'an tsaro ba sa tabuka komai a kansu; wani lokaci sai a sake su ba tare da an yi musu hukunci ba, wani lokacin ma idan aka kai hari wasu kauyukan babu jami'an tsaron kwata-kwata," a cewar Dakta Kabiru Adamu.

"Harkar tsaro kusan ita ce wajibi ga dan Adam, kuma alkawarin da ke tsakanin hukuma da dan kasa shi ne samar da tsaro amma idan aka gaza dole ne dan kasa ya dauki mataki da kansa" in ji shi.

Sai dai ya ce sauya tsarin yadda ake tafiyar da lamuran tsaro na iya kawo mafita.

"Gwamnatin tarayya ta yi katutu a harkar tsaro ita kadai kuma ga shi ba a samun biyan bukata.

"Idan ta shigar da jihohi da masarautu da kungiyoyi masu zaman kansu, sannan ta horar da hukumar 'yan sanda kuma a tabbatar da an hukunta duk wani mai laifi, za a iya samun saukin matsalar," a cewarsa.

A baya-bayan nan dai, wasu jihohin arewa maso yammacin Najeriya na fuskantar karuwar hare-haren 'yan bindiga inda ake rasa rayuka da gidaje da dabbobi.

Da yawa daga cikin hare-haren na ramuwar gayya ne tsakanin wasu al'ummomi.