Da gaske Buhari na shirin sake zuwa hutu Birtaniya?

Shugaba Muhammadu Buhari

Asalin hoton, Bashir Ahmad/Twitter

Fadar shugaban Najeriya ta karyata labaran da ke cewa shugaban kasar na shirin zuwa hutu Birtaniya.

Wata sanarwa da kakakin shugaban kasar, Femi Adesina, ya fitar ta ce labaran na kanzon kurege ne kawai.

"Ana ta watsa labarai cewa Shugaba Muhammadu Buhari na shirin tafiya Birtaniya inda zai yi kwana 20, sannan ya wuce Saudi Arabia da Austria. Wannan labarin karya ne. Karya ce kawai da wasu masu ganin baike suka kitsa."

Mr Adesina ya bukaci 'yan kasar su kauracewa yada labaran kanzon kurege.

A baya dai shugaban kasar ya je kasar ta Birtaniya, ciki har da ziyarar hutu da kuma ta jinya.

Masana sun sha tofa albarkacin bakinsu game da tafiye-tafiyen da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke yi zuwa ketare, wadanda jam`iyyar hamayya ta PDP ke zargin cewa ba su da wani amfani.

Jam'iyyar adawa ta PDP ta ce ba ta gani a kasa ba, duk da cewa bangaren gwamnati na cewa Najeriya na cin gajiyar wadannan tafiye-tafiyen.

Masana kimiyyar siyasa irin sun ce tafiye-tafiyen suna da alfanu sannan suna daga darajar kasar a fannin diflomasiyya.

Ta fannin tattalin arziki kuma a cewarsa, tafiye-tafiyen na bada kafar tattaunawa wajen ciyar da tattalin arzikin kasar gaba.

Rahotanni sun nuna cewa shugaban kasa ya yi tafiya sau kusan 100 tsakanin shekarar 2015 zuwa 2019,

Kazalika rahotannin na cewa a kiyas kwanakin da shugaban ya yi a kasashen waje a tsawon shekarun da ya yi yana mulki a kasar sun haura kwanaki 420.