Hisba ta kama mai tallan maganin kara karfin maza a Kano

Hisbah

Asalin hoton, AFP

Hukumar Hisbah ta jihar Kano da ke Najeriya ta tabbatar da kama wani matashi da take zargi da sayar da maganin gargajiya na kara karfin mazakuta.

Hukumar ta ce mutumin yana amfani da kalaman batsa wajen tallata magungunan da yake sayarwa.

Mataimakin shugaban hukumar Hisba na jihar mai kula da ayyuka na musamman, Malam Muhammad Albakari, ya shaida wa BBC cewa matashin na yin kalaman batsa kuma wani lokaci sai an runtse ido don kaucewa ganin abin da yake dagawa yana kwantace domin tallan maganin nasa.

Mai sayar da maganin na yin tallan ne a kasuwa Kofar Wambai da ke tsakiyar birnin Kano, inda yake amfani da amsa-kuwa wajen jawo hankalin jama'a.

Hukumar ta Hisba dai ta ce yanayin ko kuma kalaman da yake amfani da su wajen tallata irin wadannan magunguna basu dace ba.

Mataimakin shugaban hukumar ya kara da cewa sun kama matashin ne bayan da aka kai musu koke a kan yadda yake amfani da batsa.

Muhammad Albakari ya ce ko da suka kama shi sun kai shi ofishinsu ne inda suka yi masa nasiha da wa'azi gami da nuna masa haramcin amfani da irin wadannan kalamai.

A cewarsa, sun kira iyayensa domin a yi masa nasiha a gabansu sannan, gabanin a sake shi, a sanya masa sharadin cewa idan aka sake kama shi da irin wannan irin wanna salo na talla za a hukunta shi.

Duk kokarin da BBC ta yi don jin ta bakin matashin ya ci tura.