Cin hanci ne ya jawo Coronavirus - Magu

Ibrahim Magu

Asalin hoton, Twitter/@EFCC

Mukaddashin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC Ibrahim Magu, ya bayyana cewa yana da yakinin cewa cin hanci ne silar bullar cutar coronavirus, cutar da ta kashe sama da mutum 1700 a duniya.

Ibrahim Magu ya bayyana haka a bikin yaye sabbin dakarun hukumar EFCC wadanda aka yaye a Kaduna, ya bayyana cewa cin hanci da rashawa ita ce babbar matsalar dan adam kuma sun fi duk wata cuta ta duniya illa.

A cewarsa, yaki da cin hanci da rashawa ba abu bane mai sauki kuma cin hanci na bazuwa kamar cutar daji a lungu da sako kuma cin hanci ke jawo talauci da rashin tsaro da rashin aikin yi da karancin ilimi da kuma ababen more rayuwa marasa inganci.

Asalin hoton, EFCC TWITTER

Bayanan hoto,

Magu For Walk Against Corruption

Magu ya bayyana cewa a watanni shida da suka wuce, sun samu nasarar cafke sama da matasa 500 da ke zamba cikin aminci ta intanet kuma tuni aka maka su a kotu.

Sai dai ya bayyana cewa baza su so a tura su gidan yari ba domin akwai wani shirin da suke kokarin yi da wasu hukumomi domin gyara rayuwar matasan.

A wani bangaren kuma, Magu ya bayyana cewa a 2016 kadai, sun tura mutum 103 zuwa gidan yari, a 2017 kuma suka karu zuwa 195 sai 2018 kuma 314 a 2019 kuma 1221.