Ighalo ya kafa tarihi a Manchester United

.

Asalin hoton, Getty Images

Dan wasan gaban Najeriya Odion Ighalo ya kafa tarihi a matsayin dan wasa na farko da ya buga wa kungiyar Manchester United wasa.

Dan wasan dai ya shiga wasansa na farko da aka kara a ranar Litnin tsakanin United din da Chelsea inda United ta ci Chelsea 2-0.

Duk da cewa minti biyu zuwa uku ya buga, wannan bai hana cewa Ighalo ya cimma burinsa na zama dan wasan Najeriya na farko da ya buga wa Manchester United wasa ba.

Tsofaffin 'yan wasan Najeriya irin su Nwankwo Kanu na daga cikin wadanda suka bayyana cewa irin yadda Ighalo ke da burin buga wa United wasa wannan ba karamar dama bace la'akari da halin da kungiyar take ciki a yanzu.

Wannan tarihi ya ja hankalin masana kwallon kafa la'akari da cewa United babban kulob ne a duniya, haka ma Najeriya na daya daga cikin kasashen da kungiyar ke da dimbin magoya baya a duniya.

Sunan Ighalo na daga cikin mau'du'an da suka ja hankali kwarai da gaske a shafin Twitter sakamakon yadda aka rinka tattaunawa a kansa.

Dama tun a makon da ya gabata, sai da kocin Manchester United Ole Gunnar Solkjaer ya bayyana cewa Ighalo na cikin 'yan wasan da za su buga masa wasa a karawa da Chelsea a gasar Premier ranar Litinin.

Ighalo mai shekara 30, ya koma United daga kungiyar Shanghai Shenhua ta China inda zai yi wasa a matsayin dan wasa na aro karshen kakar bana.