'Sojoji sun kona gidaje 150 a Barikin Ladi'

'Sojoji sun kona gidaje 150 a Barikin Ladi'

Latsa alamar lasifikar da ke sama domin sauraron rahoton Raliya Zubairu

An kona gidaje da dama a samemen da ake zargin sojin kasar sun kai wa wata rugar Fulani a yankin Barikin Ladi, kamar yadda rahotanni daga jihar Filato da ke arewa ta tsakiyar Najeriya suka bayyana.

An bayyana cewa lamarin ya faru ne a safiyar Talata, kuma mazauna yankin sun shaida cewa da alama lamarin ramuwar gayya ne sojojin suka yi.

Bayanai sun tabbatar da cewa lamarin ya samo asali ne tun a ranar Lahadi bayan wasu matasa a yankin sun kai wa sojoji hari har suka kashe biyu daga cikinsu.

Alhaji Shuaibu Bayere, shi ne shugaban kungiyar Miyetti Allah na yankin Barikin Ladi ya bayyana cewa sojojin sun kona gidaje kusan "150" har da gidansa a ciki.

Mazauna yankin dai sun shaida wa BBC cewa suna cikin damuwa da zullumi sakamakon wannan abu da ya faru da su.

BBC ta nemi jin ta bakin kakakin rundunar tsaro ta hadin gwiwa da aka dora wa alhakin tabbatar da tsaro a jihar ta Filato, sai dai bai yi wani karin bayani dangane da wannan lamarin ba.

Tun a baya dai, kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun dade suna zargin sojojin Najeriya da keta hakkin bil adama wajen gudanar da ayyukansu.

Sai dai sojojin kasar sun sha musanta wannan zargi inda suke cewa zargin bai da tushe.