Yadda ‘yan bindiga suka kashe ma’aikaciyar Aso Rock

Fadar Shugaba Buhari

Fadar shugaban Najeriya ta bayyana alhininta kan kisan da aka yi wa Ms Laetitia Naankang Dagan, mataimakiyar darakta a bangaren mulki da ke Fadar Shugaban kasa.

Alhinin na kunshe cikin wata sanarwa da Attah Isa, mataimakin shugaban sashen hulda da jama'a ya sanya wa hannu.

A ranar Litinin ne aka samu labarin kisan da wasu da ake zargi 'yan bindiga ne suka yi wa Ms Dagan a gidanta da ke Abuja.

A sanarwar, babban sakatare a Fadar Shugaban Najeriyar da ke Abuja, Jalal Arabi ya bayyana kisan da aka yi wa Ms Leticia a matsayin babban rashi ga iyalanta har ma ga daukacin ma'aikatan Fadar Shugaban Kasa.

"Ma'aikaciya ce mai sadaukar da kai da aiki tukuru, kuma mun ji zafin kisan gillar da aka yi ma ta, in ji Arabi yayin wata ziyara da ya kai ga 'yan uwan mamaciyar.

Arabi ya kuma bayyana karfin gwuiwa cewa 'yan sanda za su gano wadanda ke da alhakin kisan Ms Leticia, kuma doka za ta yi halinta a kansu.

Ms Dagan mai shekara 47 'yar asalin jihar Filato ce. Ta yi aiki har kimanin karfe takwas na daren Litinin a ofishinta.

Amma da misalin karfe 11 na daren sai wasu wadanda ba a san ko suwa ne ne ba suka kashe ta a cikin gidanta.