An halatta auren mace fiye da daya a Amurka

Trump

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Yanzu mutum zai iya auren mace fiye da daya ko da yake za a ci tararsa $750.

Majalisar Dattijai a jihar Utah da ke Amurka ta kada kuri'ar halatta auren mata fiye da daya.

A baya dokar jihar ta tanaji daurin shekaru biyar a gidan yari ga duk wanda ya auri mace fiye da daya a jihar da mafi yawanci kiristoci mabiya darikar Mormons ne.

Amma yanzu mutum zai iya auren mace fiye da daya ko da yake za a ci tararsa $750.

Sai dai ana ganin dokar za ta fuskanci turjiya a majalisar wakilai.

Wakilin BBC ya ce dan majalisar da ya gabatar da kudirin dokar ya ce dokar da ke aiki a yanzu ta jefa iyalai halin kyama tare da haifar da wata al'ada ta cin zarafi.

Masu adawa dai na ganin dokar hatsari ce musamman ga mata kanana da ake tilasta wa auren masu manyan shekaru.