Me ya sa Boko Haram ke yawan kai hari garin Chibok?

  • Sagiru Kano Saleh
  • Broadcast Journalist
@

Asalin hoton, Getty Images

Mayaka dauke da manyan bindigoyi sun shiga garin da tsakar dare suka tashi mazauna da karar harbi kafin su kutsa cikin dakunan kwanan dalibai suka loda su a motoci sannan suka yi awon gaba da 'yan mata 276 zuwa inda ba a sani ba.

Karon farko ke nan da aka fara ganin irin wannan tashin hankali a garin Chibok duk da cewa kungiyar Boko Haram ta saba kai hari a wasu kananan hukumomin jihar Borno.

Wasu 'yan matan sun tsere bayan sun diro daga motocin da maharan suka loda su. Wasunsu kuma kungiyar ce ta sako su a musayar da ta yi da gwamnatin Najeriya wadda kungiyar agaji ta Red Cross ta jagoranta.

Kungiyar ta saki 100 daga cikin daliban, ita kuma gwamnatin ta saki saki wasu mayakan kungiyar da ke hannunta. Wannan harin na ranar 14 ga watan Afrilun 2014, shi ne ya fara fitar da sunan Chibok a duniya.

Kafin harin Chibok, Boko Haram ta sha kai wa makarantun boko hare-hare saboda akidarta na haramcin ilimin boko da ta ce yana gurbata tarbiyya.

Hakan ya tilasta rufe daruruwan makarantun a jihohin Yobe da Borno da Adamawa yayin da mazauna suka yi gudun hijira domin tsira da rayukansu.

A jihar Yobe mai makwabtaka da Borno, mayakan Boko Haram sun kashe mutum 50 bayan sun bude wa dalibai wuta a dakunan kwanansu da tsakar dare a makarantar koyon aikin noma da ke karamar hukumar Gujba.

Abubuwan da ke jawo karuwar hare-hare a Chibok sun hada da:

  • Muhimmancin garin Chibok
  • Dajin Sambisa
  • Rashin kayan yaki
  • Sauya salon yaki
  • Akida

Sace 'yan mata

Kasancewar kungiyar ba ta taba kai wa Chibok hari ba a wancan lokaci, ya sa mahukunta ke ganin akwai aminci da za a iya amfani da makarantar 'yan matan a gudanar da jarabawar kammala karatun sakandare.

Sace 'yan matan Chibok ya haifar da gangami mafi girma na nuna kyamar ayyukan kungiyar da fafutukar neman gwamnati ta ceto daliban daga hannun kungiyar a kafafen sada zumunta, wato #BringBackOurGirls.

Shekara shida ke nan kungiyar ba ta sako sauran daliban ba duk da cewa gwamantin kasar ta sha nuna damuwa da alkwarin yin dukkan mai yiwuwa domin sake sada daliban da iyalensu.

Ci gaban hare-hare

Asalin hoton, STEFAN HEUNIS

Ko bayan harin Chibok na farko, kungiyar ta ci gaba da kai hare-hare mafiya muni a wasu garuruwa.

Amma hare-haren da suka shafi Chibok na yawan daukar hankalin masu sharhi da kasashen duniya da kungiyoyin agaji da ma 'yan jarida fiye da sauran wurare.

Hakan ya sa ake ganin muhimmancin da ake bai wa lamarin garin Chibok ya wuce wanda ake bai wa sauran garuruwan da hare-haren kungiyar ya fi muni.

Kakakin kungiyar 'yan Chibok, Dakta Allen Manasseh ya ce daga watan Disamban shekarar 2019 zuwa watan Fabrairun 2020, kungiyar ta kai hare-hare shida a garin Kwaringilim.

Me ya sa hare-haren Chibok ke daukar hankali?

"Wannan ba ya rasa nasaba da sace 'yan matan da kungiyar ta yi a 2014 wanda yasa duniya ta san da garin," a cewar Dakta Kabir, wani manarzarcin harkar tsaro.

"Kazalika fahimtar cewa yawancin 'yan garin Kiristoci ne na kawo tausayi, musamman daga yawancin kungiyoyin agaji wadanda 'yan kasashen Turai ne, kuma yawancin kasashensu addinin Kirista suke bi.

"To duk inda ake da irin wannan matsala ko kuma ta shafi addinin Kirista to za ka ga suna ba shi muhimmanci", a cewarsa.

Muhimmancin Chibok

Tun bayan sace dalibai da kungiyar ta yi a garin yasa ta samu muhimmanci da tausayawa daga gwamnati da kasashe da kungiyoyi.

Hare-haren da ake kai wa yankin Chibok na yawan tuna wa duniya da lamarin sace daliban da kungiyar ta yi.

Hakan ya sa kungiyar ke kokarin amfani da hare-haren da suke kai wa garin domin jan hankalin duniya.

"Shi kuma ta'addanci ya ginu ne a bisa irin yada labarai. Duk abin da za su yi wanda zai taimaka musu ko ya samu karbuwa a wurin 'yan jarida a yada shi to za ka ga suna ta yi", in ji Dakta Kabir

Me ya kawo karuwar hare-hare?

A baya-bayan nan damuwa game da matsalar tsaro a Chibok ta kara dawowa bayan Boko Haram ta kai wasu hare-hare a yankin.

Dakta Kabir ya alakanta karuwar hare-haren Boko Haram a yankin Chibok da rashin isassun jami'an tsaro da kuma dajin da ya hada yankin Damboa zuwa Kwaringilim har zuwa Alagarno, inda a baya ya zama kusan wurin zaman kungiyar.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An dauki wanan hoton ranar 5 ga watan Maris din 2015, iyayen 'yan matan Chibok da aka sace ne suke jiran isar ministar kudin Najeriya ta lokacin Ngozi Okonjo-Iweala

"Wadannan wuraren kamar babu inda ma za ka je ka iske wani wuri da akwai sojoji ko ana kula da irin wadannan jejin. Wuri ne kamar suna da hanyar tafiyarsu, duk sadda suka ga dama za su iya bi", a cewar Allen.

Sannan akwai garuruwan da suka dade karkashin 'yan Boko Haram kuma har yanzu ba a je wuraren an tantance domin gano 'yan Boko Haram da ke zaune a wuraren ba", cewar Dakta Allen Manasseh.

"Idan ma an kai hari irin haka, kafin jami'an tsaron su je 'yan Boko Haram sun riga sun yi barna, sun yi awon gaba da duk abin da za su iya, sannan ba za a iya cim masu ba.

"Idan an je gari kawai sai dai a kirga yawan wadanda suka kashe da wadanda suka tafi da su da gidajen da suka kona, a kai rahoto."

Kakakin kungiyar 'yan Chibok, Dokta Allen Manasseh ya ce daga watan Disamban shekarar 2019 zuwa watan Fabrairun 2020, kungiyar ta kai hare-hare shida a garin Kwaringilim.

'Yan Chibok

Allen Manasseh ya alakanta karuwar hare-hare a yankin Chibok da rashin isassun jami'an tsaro da kuma dajin da ya hada yankin Damboa zuwa Kwaringilim har zuwa Alagarno inda a baya ya zama wurin zaman kungiyar.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Makarantar Chibok da aka kona

"Wadannan wuraren kamar babu inda ma za ka je ka iske akwai sojoji ko ana kula da irin wadannan dazukan. Wuri ne kamar suna da hanyar tafiyarsu, duk sadda suka ga dama za su iya bi", a cewar Allen.

"Sannan akwai garuruwan da suka dade karkashin 'yan Boko Haram kuma har yanzu ba a je an tantance domin gano 'yan Boko Haram da ke zaune a wuraren ba", cewarsa.

"Idan ma an kai hari irin haka, kafin jami'an tsaron su je 'yan Boko Haram sun riga sun yi barna, sun yi awon gaba da duk abin da za su iya, sannan ba za a iya cim masu ba.

"Idan an je gari kawai sai dai a kirga yawan wadanda suka kashe da wadanda suka tafi da su da gidajen da suka kona, a kai rahoto."

Rev. Enoch Mark, shi ma dan asalin garin Chibok ne, wanda ya yi zargi ci gaban hare-haren Boko Haram a kan abin da ya kira "sakacin gwamnati."

"Da a ce gwamnati ta yi niyya, ina Boko Haram suke? Sun fi karfin sojin Najeriya ne? Rashin sa kai ne, rashin sa niyya ne?

"In ba gwamnati ta sake wa Boko Haram ba, babu yadda za a yi Boko Haram su fi karfin sojin Najeriya."

Masana harkar tsaro

BBC ta kuma nemi jin dalilin da ya sa kungiyar Boko Haram ta kai hare-haren a yankin Chibok a baya-bayan nan daga Dokta Kabir Adamu, shugaban cibiyar nazarin tsaro ta Beacon Consulting a Najeriya.

Daga cikin abubuwan da ya bayyana a matsayin wadanda suka haifar da hare-haren kungiyar a yankin akwai:

Sauya salon yaki

Sakamakon hare-haren da kungiyoyi Boko Haram da ISWAP suka kai wa kananan sansanonin sojin kasar har suka mamaye 18 daga cikinsu bayan sun kashe sojoji sun kwace makamai, rundunar ta sauya salonta na yin yaki da kungiyar.

Rundunar ta rufe kananan sansanoninta (Forward Operation) ta maye gurbinsu da manya (Super Camps).

Amma wasu kwararru na ganin gazawar sabon salon saboda yana rage wa sojoji damar na kare mazauna yankunan, a cewar Dokar Kabir.

"A baya, garuruwan da ke arewa da jihar Borno irin su Rann da Kalabalge akwai kananan sansanonin soji, amma kusan dukkansu 'yan kungiyar sun mamaye su.

"Kusan 80% na makaman da suke amfani da su suna samunsu ne daga sansanonin sojin da suka mamayewa. Don haka sabon tsarin da rundunar ta fitar abu ne mai muhimmanci.

"Sai dai kuma kafa manyan sansanonin ya haifar da wani gibi sakamakon karancin makamai da sojoji da su kansu manyan sansanonin da aka kafa.

"Akwai alkaluman da ke nuna cewa tsakanin sansanoni 18 zuwa 19 ne aka kafa, alhali kamata ya yi a kafa akalla guda 35 a jihar Borno saboda girmanta.

"Barin wasu wuraren babu wadannan sansanoni soji ya bai wa mayakan damar yawo suna kai hare-hare."

Rashin kayan yaki

Dakta Kabiru ya kuma: "Saboda rashin ingancin kayan aikin da sojojin ke amfani da su, da wuya a samu sojojin Najeriya na yawo da dare suna kare garuruwan da ke yankin.

"Shi yasa maharan ke yawan amfani da damar wurin kai hare-hare a cikin dare", a cewarsa.

Kazalika rashin ingantattun hanyoyin sadarwa da rashin hadin gwiwa tsakanin sansanonin da rundunoni da kuma rashin damar ba da agaji a cikin lokaci a yankin.

"Na farko shi ne ingancin hanyar sadarwar ta yadda sansanonin za su iya tuntubar juna domin neman gudunmuwa ko kai wa garuruwa agaji idan an kai hari.

"Na biyu shi ne damar iya kai dauki a kan kari, amma rundunar sojin kasar na da rauni a wannan bangarorin - babu isassun motoci da jiragen sama da kuma hanyoyin sadarwa".

"Akwai kuma rashin hadin kai tsakanin rundunar sojin kasa da ta sojin sama. Da akwai hadin kai, da rundunar sojin kasa za ta iya tuntubar rundunar sojin sama, ita kuma za ta kawo agaji ko ta kai hari cikin dan lokaci," in ji Dakta Kabiru.

Muhimmancin Chibok

Shaharar da garin Chibok ya samu a wurin kasashe da kungiyoyi da 'yan jarida tun bayan sace dalibai mata na daga cikin dalilan kungiyar na kai wa yankin hari domin yin farfaganda.

Da zarar sun kai hari a garuruwan da aka damu da su, hankula kan tashi kuma hakan na saurin nuna cewa kungiyar na da karfi.

"Kasancewa Chibok a jihar Borno da kuma sace 'yan matan nan da aka yi a baya, wadda maganar ta karade duniya cewa an sace dalibai mata kuma an ba shi muhimmaci.

"To ka ga siyasa ta shigo ciki ke nan ta yadda yau idan suka kai hari a garin, yadda kungiyoyi da 'yan jaridu za su dauki maganar zai fi idan suka kai hari a wani wuri.

"Shi kuma ta'addanci ya ginu ne a bisa irin yada labarai. Duk abin da za su yi wanda zai taimaka musu ko ya samu karbuwa a wurin 'yan jarida a yada shi to za ka ga suna ta yi," in ji Dokta Kabir.

Dajin Sambisa

Asalin hoton, environment and society portal

Bayanan hoto,

Hoton yadda Dajin Sambisa yake a 2017

Kusancin Chibok da dajin Sambisa, daya daga cikin manyan mafakar Boko Haram hudu, na bai wa mayakan damar fitowa cikin dare su kai harin sari ka noke.

"Wurare uku ne dama kungiyoyin suke fakewa... da kuma shi kansa Dajin Sambisa, yawanci daga nan ciki suke fitowa su kai irin wadannan hare-haren, sai su koma.

"Ba shakka kasancewar Chibok kusa da shi wannan dajin yana ba su dama su boye, sannan su fito su kai hare-hare da dare sannan su koma su boye."

"Abin da nake so in nuna shi ne mazauna yankin ne, sun san yankin, sun san duk wani abu da yankin ke tattare da shi, sun san inda za su buya, kuma kafin mazauna su fara daukar mataki daga baya ai a cikin gari suke zaune tare da mutane."

Akida

Babu shakka galibin 'yan garin Chibok mabiya addinin Kirista ne.

"Sun san cewa idan suka je garin suka kama mutane yadda suka saba, suka tilasta musu shiga Musulunci, mai yiwuwa su samu cimma burinsu na akidar da suke ikirari.

"Kazalika za a yi ta yayata abin a duniya ta fuskar addini," kamar yadda ya kara da cewa.

Shin ana zuzuta hare-haren Chibok?

Dakta Kabiru ya ce asiyasar duniya, duk inda aka samu matsala tsakanin addinin Musulunci da Kirista za ka ga an fi yayata shi.

"Sannan idan ya shafi jinsi za ka ga shi ma ana yayata shi," a cewar masanin.

Ya kara da cewa, "Dalili shi ne yawancin su kungiyoyin agaji asalinsu da hedikwatocinsu kasashe ne na Kirista. To abin daya shafi Kirista ana yawan yayata shi".

'Iyakarta a fatar baki ne'

Duk da haka Allen ya ce maganganun da kasashe da kungiyoyin agaji ke yi na nuna damuwa a kan matsalar tsaro iyakarta kafafen yada labarai.

"Tun da aka fara magana a kan Chibok har zuwa yanzu da kyar za a samu daidai da kungiyar agaji daya da ke shiga Chibok ta yi aiki. Y

"Yawancin ayyukan da ake yi a wasu wurare ne, ba sa ma isa Chibok din.

"Makarantar nan da aka kona kusan shekara shida ke nan, har yanzu ba a kammala gyaranta an ci gaba da aiki da ita ba," a cewar Allen Manasseh.