Wane ne gwamnan Borno Babagana Umara Zulum?

.

Asalin hoton, Babagana Umara Zulum/Facebook

A ranar Laraba 29 ga watan Mayun 2019 ne aka rantsar da Babagana Umara Zulum a matsayin gwamnan jihar Borno, bayan ya ci zabe karkashin jam'iyyar APC, inda ya gaji Kashim Shettima.

Jama'a da dama sun yi shaidar Babagana kan cewa ba mutum ba ne wanda yake son kyalkyalin kayan duniya ko kuma tara makudan kudi, ganin irin damar da ya samu ta tara abin duniya a matakai daban-daban bayan ya sha gwagwarmayar rayuwa.

A baya-bayan nan tauraruwar gwamnan na haskawa a Najeriya, inda ake yawan yabon sa da jajircewa da nuna tausayin talaka, musamman halin da mutanen jiharsa ke ciki sakamakon rikicin Boko Haram.

Shin wane ne Babagana Umara Zulum? BBC ta yi nazari kan tarihinsa.

Rayuwarsa

An haife shi a ranar 26 ga watan Agustan 1969 a karamar hukumar Mafa ta jihar Borno, kuma ya yi karatunsa na firamare da sakandare a garuruwan Mafa da Monguno tsakanin 1975 zuwa 1985.

Tun a lokacin da yake dan aji biyar a sakandare, Babagana ya bayar da himma wajen fara daukar nauyin karatunsa.

Domin haka ne ya shiga sana'ar tukin mota a 1984 inda ya shafe kusan shekaru 16 yana wannan aiki.

Ya ci gaba da sana'ar tukin mota har ya je jami'a ya fara aikin gwamnati yana wannan sana'a.

Ya tuka mota nau'in tasi zuwa kirar bas da kuma a-kori-kura ta daukar itatuwa, kuma da tukin motar ne ya ci gaba da daukar nauyin karatunsa.

A shekarar 1986, Zulum ya samu gurbin karatu a kwalejin kimiyya da fasaha ta Ramat da ke Maiduguri domin karantar fasahar ban ruwa da noman rani.

Zulum na tafiyar kusan kilomita takwas daga Unguwar Kofa Biyu zuwa makaranta a duk lokacin da yake da aji.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Domin kara samun kudi don tallafa wa karatunsa, Babagana Zulum ya fara sana'ar markade a ranakun Asabar da Lahadi.

Ya kammala karatunsa na difloma a 1988 inda kuma ya fara aiki a ma'aikatar noma ta jihar Borno tsakanin 1988 zuwa 1989, sa'annan ya koma hukumar kananan hukumomi ta Borno State Unified Local Government Service a jihar.

Duk da cewa ma'aikacin gwamnati ne a wancan lokaci, hakan bai hana shi tukin mota ba har zuwa lokacin da ya samu gurbin karatu a Jami'ar Maiduguri domin karanta fasahar noma wadda ya kammala a 1994.

Saboda son ganin ya samu karatun boko ingantacce, ya tafi Jami'ar Ibadan inda ya yi digiransa na biyu kan fasahar noma.

Sai dai kafin fara digiri na biyu, sai da ya jinkirta rijistar zangon karatunsa inda ya dauki makonni uku domin yin kabu-kabu da mota domin samun kudin rijistar zangon karatun.

Ko da ya kammala karatun a 1998, ya dawo a matsayin ma'aikacin gwamnatin jihar a matakin babban injiniyan noma a jihar.

Ko a lokacin da ya dawo aikin gwamnati, ya fara koyarwa a Jami'ar Maiduguri kuma a wannan jami'a ce ya kammala digirinsa na uku kan kasa da fasahar ruwa ( Soil and Water Engineering) a shekarar 2009.

Muhimman abubuwa game da Zulum

  • Ya yi sana'ar saka tiles yana yaro karami tare da mahaifinsa
  • Ya shafe shekaru 16 yana tukin mota a matsayin direban tasi da kuma daukar itace
  • Ya yi sana'ar markade lokacin da yake karatun difiloma
  • A lokacin da yake firamare, yana tafiyar kilomita bakwai zuwa makaranta

Asalin hoton, Babagana Umara Zulum/Facebook

Siyasa

Ganin irin jajircewar Babagana da kuma tsawon tarihin da ya kafa kokari a wajen aiki da kuma rike gaskiya, tsohon gwamnan Borno a wancan lokaci Kashim Shettima ya zabi Babagana domin ya zama shugaban kwalejin kimiyya ta Ramat.

Sai dai ko a lokacin da aka ba shi wannan mukami, Farfesa Babagana ya shaida cewa ba zai karbi wani albashi ba a matsayin shugaban jami'a, zai ci gaba da karbar albashinsa a matsayinsa na malamin makaranta.

Gwamna Kashim Shettima ya ba shi kwamishina mai lura da sake gina yankin da Boko Haram suka lalata, saboda nagartarsa da ya gani.

Tun daga wannan lokaci Zulum ya dukufa da aikin da ya rataya a wuyansa har kuma ya samu nasarar sa ido wajen gina dubban gidaje da za su kwashi dubban 'yan gudun hijira.

Ko a lokacin da jam'iyyar APC ta ayyana Babagana Umara Zulum a matsayin wanda zai tsaya takararta ta gwamna a 2019, ya riga ya yi suna a jihar ta Borno bisa tarihin da ya kafa na jajircewa wajen aiki da rikon amana.

Asalin hoton, @PROFZULUM

Bayanai: Daga gwamnatin jihar Borno