An kai sabon hari a Chibok

.

Asalin hoton, Getty Images

Wasu mahara da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne sun kai hari a garin a Kwaringilim da ke karamar hukumar Chibok a jihar Borno.

An bayyana cewa maharan sun kutsa garin a motoci da babura, tare da kona wata makarantar firamare.

Tun a lokacin da suka shiga garin, mayakan suka soma bude wuta a wata kasuwar garin na Kwarangilim tare da wawashe kayan abinci, har ma da wasu raguna da aka ce sun yi awon gaba da su.

Hakan ne ya sa jama'ar garin tserewa zuwa cikin daji domin tsira da rayuwarsu.

BBC ta tuntubi Manjo-Janar Olusegun Adeniyi wanda shi ne kwamandan rundunar wanzar da zaman lafiya ta Operation Lafiya Dole kuma ya tabbatar da kai harin.

Adeniyi ya tabbatar da cewa dakarunsu sun hana maharan shiga cikin garin kamar yadda suka so.

Karamar hukumar Chibok dai ta yi kaurin suna wajen fama da hare-haren yan kungiyar Boko Haram a jihar Borno.

Jama'a da dama a fadin duniya sun san da garin ne bayan sace dalibai 'yan mata 276 da 'yan kungiyar Boko Haram suka yi a shekarar 2014.

Lamarin ya janyo Allah wadai daga sassan duniya daban-daban, ko da yake daga bisani gwamnatin Najeriya ta kubutar da da yawa daga cikin su.