Mutanen Borno za su yi azumi kan Boko Haram

.

Asalin hoton, @PROFZULUM

Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya bayyana ranar Litinin 24 ga watan Fabrairun 2020 a matsayin ranar da za a gudanar da azumi da addu'o'i domin neman sauki kan Boko Haram.

Ya bayyana haka ne yayin wani jawabi na minti shida da yayi wa jama'ar jihar a ranar Laraba.

Sai dai gwamnan ya ce ba wai ranar hutu bace domin za a je aiki a ranar Litinin din.

Ya bayyana cewa wasu za su ga wannan lamarin kamar wani sabon salo, amma hakan ya zo ne sakamakon kiraye-kirayen da jama'a ke yi na yin hakan.

Ya shaida cewa a matsayinsa na gwamnan jihar, zai yi azumi ranar Litinin kuma ya yi kira ga kowa yayi hakan.

Haka zalika, gwamna Zulum ya yi kira ga 'yan uwa da abokan jihar da su yi azumi a ranar domin dawowa da zaman lafiya a jihar.

Gwamnan ya shaida cewa tuni Shehun Borno ya tabbatar masa cewa duka limamai na kananan hukumomi 27 da ke jihar za su yi addu'o'i da Qunuti a duka salloli biyar na ranar Litinin.

Ya kuma ce shugabannin Kiristoci a jihar sun yi masa alkawarin yin addu'o'i na musamman a coci a ranar.

Gwamnatin Buhari dai ta dade tana ikirarin karya lagon kungiyar Boko Haram da ta addabi yankin arewa maso gabas, amma kuma har yanzu mayakan kungiyar na ci gaba da yi wa mutanen yankin barazana.

Ko a kwanakin baya sai da 'yan kungiyar suka kai hari a Auno da ke jihar ta Borno inda suka kashe fiye da mutane 30.

Lamarin dai ya jawo ce-ce-ku-ce daga jama'a da dama har da kungiyoyi masu zaman kansu.