Kotu ta bayar da umarnin mayar wa Dasuki fasfonsa

Dasuki

Asalin hoton, Getty Images

Wata babbar kotu da ke Maitama a Abuja, babban birnin Najeriya ta bayar da umarnin mayar wa tsohon mai bai wa shugaban kasa shawara kan lamuran tsaro, Kanar Muhammad Sambo Dasuki mai ritaya fasfonsa.

Kotun karkashin alkali Hussein Baba-Yusuf ce ta umarci magatakardan kotun da ya mika wa Dasuki fasfo din ta hannun lauyansa domin sabunta takardar saboda wa'adinsa ya riga ya cika tun bayan da kotu ta kwace fasfo din.

Umarnin kotun zai bai wa Dasuki damar samun biza domin zuwa asibiti bayan shekara hudu da ya yi tsare a hannun hukuma.

Dasuki da wasu mutum hudu suna fuskantar shar'a ne a kotun bisa zarginsu da cin amana da kuma almundahana.

Matakin alkali Baba-Yusuf ya zo ne bayan wata kara da lauyan Dasuki, Mr Ahmed Raji ya shigar bisa sashe na 1 da 2 da 491 da kuma 492 na dokar hukunta manyan laifuka ta 2015.

Da yake yanke hukunci kan karar ta Dasuki, alkalin ya ce tun da EFCC bata kalubalanci batun ba, ya kamata a amince da ita.

An kuma sanya ranar 13 ga watan Maris din 2020 a matsayin ranar da za a saurari shari'a kan tuhume-tuhumen.

A watan Disambar 2019 ne gwamnatin Najeriya ta saki Kanar Sambo Dasuki.

An sake shi ne bayan sakin dan fafutuka mai jaridar nan ta Intanet, Sahara Reporters, Omoyele Sowore.

Kafin sakin nasu gwamnatin ta ja kunnen mutanen biyu da su guji aikata abubuwan da za su janyo tayar da zaune tsaye da kuma cikas ga tsaron kasa sannan kuma ka da su yi tarnaki ga shari'ar da ake yi musu bisa dokokin kasa.

A karshen shekara ta 2015 ne gwamnati ta kama Sambo Dasuki bisa zargin karkatar da kudin makamai sama da dala biliyan biyu lokacin gwamnatin PDP, ta Goodluck Jonathan.

A baya dai kotu ta sha bayar da belin Sambo Dasukin, amma gwamnati ta ki sakinsa.