Chloroquine na maganin coronavirus

Coronavirus

Asalin hoton, Science Photo Library

An gano cewa maganin zazzabin cizon sauro na Chloroquine phosphate wanda aka fi amfani da shi a nahiyar Afirka musamman a shekarun 1980 da 1990 yana warkar da cutar numfashi ta coronavirus.

Ma'aikatar kimiyya da fasaha ta kasar China ce ta bayyana hakan ranar Laraba.

Gidan talbijin na China Global Television Network ya ruwaito cewa daukacin masana a kasar sun amince a yi amfani da Chloroquine phosphate domin maganin cutar Covid-19 virus, wadda aka fi sani coronavirus.

An dade ana amfani da maganin wurin magance zazzabin cizon sauro gabanin sauron ya soma bijire wa maganin.

Kafar watsa labaran kasar ta Xinhua ta ruwaito cewa an yi gwajin chloroquine a fiye da asibitoci goma da ke Beijing, babban birnin kasar China da wasu larduna biyu, "kuma yana aiki sosai".