'Majalisar dokokin Najeriya na fuskantar barazanar tsaro'

Majalisar dokokin Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

'Yan majalisar dokokin Najeriya sun ce suna fuskantar barazanar ta'addanci, sakamakon zaman da ake yi kara-zube a majalisun dokokin kasar.

Wannan ne ya sa 'yan majalisar suka fara wani yunkuri na tsaurara tsaro a mashigun majalisar tare da samar da kayan aiki irin na zamani, ciki har da kemarar tsaro.

Sanata Abdullahi Yahaya shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, ya shaidawa BBC cewa majalisar ta koma ba shamaki kowa na iya shiga.

"A halin da ake ciki yadda ba ka sanin wanda ke shiga da fita, komi na iya faruwa, ana iya taba lafiyar 'yan majalisa," in ji shi.

Bangaren Akawun majalisar dokokin ya tabbatar da kalubalen da jami'ansu ke fuskanta wajen sa-ido akan masu shiga majalisun dokokin, wadanda ba s u gaza dubu hudu zuwa biyar a kowace rana. ciki har da matsalar masu shiga da katin jabu.

Sai dai ana ganin mamayar da 'yan maula da wasu `yan talla ke yi wa majalisar na cikin dalilan da suka sa `yan majalisar suka fara damuwa.

Amma Hon Sada Soli Jibia ya ce matakan tsaron ne suka tabarbare, dalilin da ya sa majalisa ta ga ya zama wajibi a tsaurara matakan tsaro.

Tuni aka fara daukar matakan ba-sani-ba-sabo kan ma'aikata da baki da ke ziyartar majalisa, inda sai wanda ya nuna katin shaidar shiga ko wata takardar izini kafin ya samu shiga majalisar.

Majalisar dokokin Najeriyar dai na wannan koken ne yayin da ake kukan matsalar tabarbarewar tsaro a sassan kasar, musamman ma shiyyar arewa-maso-gabashin kasar, da ke fama da hare-haren Boko Haram.

Da kuma yankin arewa maso yammaci da ke fama da hare-haren 'yan bindiga da masu satar mutane domin kudin fansa.