Dan bindiga ya kashe mutane da dama a Jamus

An gano gawar mutumin da ake zargi da kai harin a gidansa tare da gawar mahaifiyarsa.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

An gano gawar mutumin da ake zargi da kai harin a gidansa tare da gawar mahaifiyarsa

Wani dan bindiga ya bude wuta a wurare biyu da ake sayar da shisha a birhin Hanau da ke Yammacin Jamus, inda ya kashe akalla mutum takwas kana ya jikkata mutane da dama, a cewar 'yan sanda.

A dukkan wuraren biyu da aka kai wa hari ranar Laraba, rahotanni sun ce akasarin masu zuwa mashayar Kurdawa ne.

An gano gawar mutumin da ake zargi da kai harin a gidansa tare da gawar mahaifiyarsa.

Masu shigar da kara na gwamnatin tarayya sun ce harin na ta'addanci ne, yayin da jami'ai suka ce akwai shaidun da ke nuna cewa maharin mai tsattsauran ra'ayi ne.

'Yan sanda sun ce mutumin da ake zargi da kai harin ya harbe kansa.

Jaridar The Bild ta ruwaito cewa mutumin dan kasar Jamus ne wanda aka bai wa lasisin amfani da makamai, tana mai cewa an gano harsasai da jigidar bndiga a cikin motarsa.