'Yan Najeriya da India sun yi fim kan soyayya

Image copyrightINSTAGRAM/RUSLAANMUMTAZ

Asalin hoton, Image copyrightINSTAGRAM/RUSLAANMUMTAZ

Wani fim mai suna 'Namaste Wahala' da aka hada gwiwa wajen shirya shi tsakanin taurarin fina-finan Indiya da takwarorinsu na Najeriya ya ja hankalin 'yan kallo.

Za a soma nuna fim din ne ranar 24 ga watan Afrilun 2020.

Tauraruwa Ini Dima-Okojie da tauraron fina-finan Indiya Ruslaan Mumtaz sun yi fim din "wanda yake bayar da labarin wasu masoya da ke nuna al'adun kasashen biyu".

Fim din ya ja hankalin masu kallo inda suka yi ta tsokaci.

"Fina-finan Najeriya sun hada gwiwa da na Indiya? Wannan abu ya yi armashi, kuma shi ne fim irinsa na farko," a cewar wani mai amfani da Twitter.

Sauran taurarin da za su fito a fim din sun hada da; Richard Mofe Damijo da Joke Silva da Osas Ighodaro da mai barkwancin nan broda shaggi da mawaki M.I Abaga da dai sauran su.

Wanda ya bayar da umarni a fim din ya ce an dauki fim di ne a Najeriya da Indiya.