'Yadda mijina ya watsa min asid ya lalata min jiki'

  • Daga Hailu Sahle
  • BBC Tigrinya
Menbe Aklilu tare da Atsedea asibiti

Asalin hoton, Menbere Aklilu

Bayanan hoto,

Menbere Akilu ta shirya yadda za ta kai Atsede Nguse Amurka domin ayi mata magani

Wata mata 'yar kasar Habasha da mjinta ya lalata wa fuska bayan ya watsa mata asid a shekarar 2017, ta ce duk da halin da take ciki tana mai nuna godiyarta.

Ta shaida wa BBC cewa "Akwai mutanen kirki a duniya haka ma akwai marasa kirki".

Ta ci gaba da cewa "Irin kirki da kaunar da mutane suka nuna mini bayan an watsa mini asid ya sanya ni godiyar Allah."

Atsede Nguse 'yar kimanin shekara 29 wadda kuma uwa ce, ta ce asid din da aka watsa mata ya bata mata fuska da jikinta.

Ba za a iya yi mata magani a kasarsu ba kuma ba ta ma da kudin maganin.

Asalin hoton, Atsede Nguse/Menbere Aklilu

Bayanan hoto,

Ms Atsede kafin da kuma bayan an watsa mata asid

Bayan da 'yan uwa da kawaye da kuma abokan arzikin suka samu labarin abin da ya faru da ita, sai suka hada kudi suka biya mata don a yi mata tiyata a Thailand.

To amma sai kudin ya kare kafin a gama yi mata maganin dole ta koma gida.

Yanzu kuma a karo na biyu wata baiwar Allah ta zo domin ta taimaka mata.

Menbere Aklilu, wata 'yar kasar Habasha mai fafutukar kare 'yancin mata da ke zama a Amurka, ta karanta abin da ya faru da Ms Atsede a Facebook.

A matsayinta na wadda ta taba fuskantar cin zarafi daga wajen mjinta, sai ta ce zata taimaka wa Ms Atsede.

Ta ce "Da na karanta labarinta, sai na tausaya mata, amma kuma da na fahimci uwa ce, sai na ce idan da dana ne ya tsinci kansa a wannan halin fa?"

"Gaskiya wannan abu ya sosa mini zuciya" in ji Menbere Akilu.

Wata kungiya mai zaman kanta ta Birtaniya ta kiyasta cewa, ana watsa wa mata 50 zuwa 75 asid a Habasha a kowacce shekara.

Wannan matsala kuma ta samo asali ne daga rikicin cikin gida.

Wani bincike da gwamnatin Habasha ta yi a 2016, ya ce fiye da kaso uku cikin 100 na matan da suka yi soyayya, to suna fuskantar cin zarafi kala-kala daga wajen samarin nasu.

A bangaren Ms Atsede, sun yi aure ne da mijinta a 2012, kuma mijinta ya kan da ke ta a kan dan abin da bai taka kara ya karya ba.

Ta ce "Makotanmu su kan damu, har sukan ce idan ban yi hankali ba, wata rana sai ya kashe ni, amma duk da haka na ci gaba da zama da shi saboda dana, saboda ba na so ya tashi ba tare da mahaifinsa ba".

Asalin hoton, Atsede Nguse

Bayanan hoto,

Ms Atsede tare da danta

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Daga karshe a shekarar 2015, bayan mijinta ya mata dukan tsiya har ya cire mata hakora ga kuma fuska a kumbure, sai ta hakura ta bar mijin nata Gambella, ta koma garinsu.

Ta ce "Bayan na koma garinmu Adirat, mahaifiyata da kuma yayata wadanda ke zaune a Saudiyya, suka taimaka mini na bude shagon kayan kwalliya, nan komai nawa ya koma dai-dai ina kuma ciniki sosai.

Sai a 2017, mijin nata ya dawo mata inda yake kiranta a waya suna gaisawa, ya kuma nuna mata kamar ba ya kasar.

Ta ce "Ya rinka nunawa kamar daga Saudiyya ya ke kira na, amma sai na fahimci karya yake saboda rannan sai na ji yara na magana da yarenmu na Tigrinya".

Ms Atsede ta ce "Da wata ya zagayo, sai ya zo gidanmu, amma sai ya rinka buya bai san na ganshi ba, ya rinka matsowa inda nake ban aune ba sai na ji ya watsa mini wani abu a fuskata".

A nan ne asid din ya kona mata fuska mata.

Ms Atsede, ta samu rauni sosai a fuskarta da hannayenta da kirjinta da kafarta daya, kuma ta rasa ganinta.

A woman who has survived an acid attack
Menbere Aklilu
I have completed a Braille course and I am learning computers. I have big dreams, and I know I am going to make it"
Atsede Nguse
Acid attack survivor

Wani abun tausayi shi ne bayan da aka kai mata danta dan shekara biyar asibiti ya ganta abin da ya biya dole ya sosa wa duk wata uwa rai.

Ta ce: "'Yan uwana sun sun kawo mini dana, ko da ya shigo dakin da nake kwance sai aka ce masa ka je ka gaishe da mamanka, sai kawai ya kalle ni ya ce ba mamansa ba ce don shi mamansa kyakkyawa ce".

Daga karshe Ms Menbere ta neme ta, ta same ta sannan ta yi kokari ta zo ta ganta, amma ta sha wuya kafin ta fita da ita zuwa Amurka.

An hada mata kudi sosai domin a yi wa Ms Atsede, magani a Amurka.

Menbere Aklilu
I help women because I love myself. Because every time you help someone, your own wound heals"
Menbere Aklilu
Women's rights activist

Mai fafutukar ta ce ta sa an yi wa Ms Atsede, magani ne kamar 'yar da ta haifa a cikinta, ta ce sun zauna tare a lokacin sun kuma gaya wa juna matsalolinsu da kuma abubuwan da suka faru da su a rayuwarsu.

Mai fafutukar ta ce "Ina taimaka mata saboda ina son kaina, sannan kuma idan har ka taimaka wa wani to shakka babu kai ma a gaba za ka samu mai taimakonka".

Yanzu Ms Atsede, ta fara samun sauki sosai, kuma tana samun taimako daga wata kungiya ta Medics da ke California, sannan kuma ta kuduri aniyar komawa ta ci gaba da rayuwarta kamar da.

Ms Atsede ta ce "An yi mini tiyata cikin nasara, ba ni da fatar saman ido, amma kuma a yanzu ina bude idona na kuma rufe, sannan kuma ina fatan nan gaba ganina ma zai dawo".

Yanzu haka dai an yanke wa mijinta hukuncin daurin rai da rai.

Ta ce "Da za a ce zan ganshi a yanzu, tambaya daya zan yi masa ita ce 'Me ya sa ka yi mini haka?".

Za ku so kallon wannan bidiyon na kasa

Bayanan bidiyo,

Wasu da aka watsa wa asid a Uganda suni yi magana da BBC kan abin da ya same su