Abin da Sarki Sanusi II ya fada a taron sake fasalin iyali a Musulunci

Sarki Sanusi II

Asalin hoton, FADARKANOTADABO

Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya yi kira ga gwamnonin jihohin Najeriya da su kirkiro da wata doka wacce za ta rage yawan mace-macen aure, da kuma kawo karshen fitintunun aure a tsakanin 'yan kasar.

Mai martaba sarkin na magana ne yayin wani taro mai taken "Sake Fasalin Zamantakewar Aure Domin Cigaban Najeriya," da aka yi a Abuja ranar Alhamis.

Mai taimaka wa shugaban kasar kan shafukan sada zumunta, Bashir Ahmad, ya bayyana a shafinsa na Twitter cewa: "Taron na kasa kan sake fasalin iyali a Musulunci domin ci gaban kasa wanda Majalisar Koli ta addinin Musulunci da hadin gwiwar Gidauniyar Aisha Buhari ta Future Assured suka shirya."

Taron ya samu halartar Shugaba Muhammadu Buhari da gwamnoni da malaman addini da sarakuna da sauran masu ruwa da tsaki.

Sarki Sanusi shi ne wanda ya fi shafe tsawon lokaci yana jawabi, wanda da alama ya ja hankalin mahalarta taron.

Shawarwarin da Sarki Sanusi ya bayar

1. Sarki Sanusi ya yi kira da a samar da wata doka da za ta sanya miji barin gidansa ga matarsa da 'ya'yansa a duk lokacin ya sake ta, a maimakon ita ta fice ta bar gidan kamar yadda aka saba a al'ada.

2. Samar da dokokin da za su kawo karshen matsalar mutuwar aure da ta zamowa kasar gagarumar matsala, musamman ma a yankin arewaci.

Sarkin ya ce ''Shin gaskiya ne uba na da damar yi wa 'yarsa aure ba tare da izinin ta ba? Shin gaskiya ne kana da damar dukan matarka?

"Shin gaskiya ne kana da damar ka haifi 'ya'ya ka watsar da su a kan titi suna bara?

"Amsoshin wadannan tambayoyi na nan a cikin Al-qur'ani da hadisai, ba ka da damar yin haka, wannan aiki ne na sarakunan gargajiya da jagororin addinai su tashi tsaye wajen fadakar da jama'a kan cewa ga abin da yake shi ne adalci,'' a cewar Sarki Sanusi.

3. Wani abu da sarkin ya mayar da hankali akai shi ne dalilin da kan janyo mutuwar auren, da ya ce dole ne malamai da jagororin al'umma su tashi tsaye, wajen ankarar da jama'a a kansu.

''Zan iya kai wa shekara 100 ina jaddada cewa ba dai-dai ba ne mutum ya rika dukan matarsa, gwamnoni, da 'yan majalisa ne ke da damar yin doka, ita kuma kotu da 'yan sanda su tsaya kai da fata wajen ganin wacce mijinta ya dake ta ta samu adalci.

"Mu sarakuna ba za mu iya haka ba, malaman addini ma ba su da damar yin hakan, idan kuwa ka saki matarka, kai ka fice ka tafi gidan iyayenka, ita ta yi zaman ta a gidan, kai ya kamata ka sama mata duk abinda take bukata.''

Wasu mahalarta taron

Wasu daga cikin mahalarta taron da suka hada da Oni na Ife, Mai Martaba Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi, ya ce an jima ana ruwa kasa tana shanyewa, don haka lokacin maganar fatar baki ya wuce.

Ya kara da cewa kamata ya yi a yanzu mahukunta su fara daukar tsauraran matakai kan dukkan wadanda aka samu da laifin cin zali da sunan aure.

Ya ce: "Maganganun baki sun isa haka, ina farin ciki shugaban majalisar dattawa yana nan. Muna bukatar daukar wannan batun da matukar muhimmanci, muna bukatar yin dokoki da za su tilasta wa iyaye lura da 'ya'yansu.

Ya ma kamata duk matakin da za a dauka a hada shi da lambar banki ta BVN ta irin wadannan iyayen da ke haifo 'ya'yan da ba a bukatar su, wadanda suke zama alakakai a cikin al'umma.

Idan ma ba za a iya kwace musu dukiya ba, to a kwace musu asusun ajiyarsu na banki. A kuntatawa rayuwarsu, har su yi abinda ya kamata, ta yadda za mu ringa samun 'ya'yan da muke bukata."

Shi kuwa gwamnan Filato Simon Bako Lalong wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin arewacin Najeriya ya ce maganganun da sarakuna suka yi a wajen, sun sa sun samu makama, kuma a yanzu babu wani gwamna da yake da uzurin kin daukar matakin da ya kamata.

Gwamna Lalnong ya ce: "Wadannan su ne abubuwan da muke tattaunawa a taronmu na gwamnonin Arewa.

"Amma duk lokacin da muka zo maganar aiwatarwa sai gwamnoni su ringa korafin cewa, idan ba su samu goyon bayan sarakuna da malaman addini ba, to akwai matsala.

"A yau ina farin cikin Sarkin Kano da Sarkin Musulmi sun fadi matsayarsu, a yanzu ina jiran malam addini, ku duba yanayin kasar nan.

"Mun riga mun yanke hukunci cewa za mu yi taro na kwanaki biyu a Kaduna a kan wannan batu. Magana ce kawai ta aiwatarwa. Bari mu ga wane gwamna ne kuma yanzu zai ce ba zai iya aiwatarwa ba."

Najeriya dai na daya daga cikin kasashen da suka fi fama da mutuwar aure a duniya kamar yadda wadanda suka gabatar da jawabai a yayin taron suka bayyana.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da mai dakinsa Aisha Buhari na daga cikin manyan da suka albarkaci taron, ba ya ga shugaban majalisar dattawan Najeriya da gwamnoni dama.