Kalli matar da aka yi wa tiyata a kwakwalwa tana kada goge

Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Wata mara lafiya a Asibitin Kwalejin Kings da ke Landan ta kada goge a lokacin da likitoci suke mata tiyata a kwakwalwa don cire mata tsiro.

Dagmar Turner, mai shekara 53, ta kada gogen ne don likitoci su tabbatar da cewa sauran sassan kwakwalwar da ke sa hannaye yin aiki ba su tabu ba a yayin tiyatar.