EFCC ta kama dan gidan tsohon gwamnan Kogi Abubakar Audu

Ta ce za a gurfanar da Muhammad Audu a gaban kuliya da zarar an kammala bincike akansa.

Asalin hoton, EFCC

Bayanan hoto,

EFCC ta ce za a gurfanar da Muhammad Audu a gaban kuliya da zarar an kammala bincike akansa.

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa, EFCC, ta ce ta kama dan gidan tsohon gwamnan jihar Kogi, marigayi Prince Abubakar Audu.

EFCC ta shaida wa BBC ranar Alhamis cewa jami'anta sun kama Muhammed Audu bisa zarginsa da aikata zamba.

"An kama mutumin da ake zargi ne ranar Talata, 18 ga watan Fabrairu, 2020 bisa zargin karkatar da miliyoyin dalar Amurka da kuma biliyoyin naira na gudunmawar da aka bai wa hukumar kula da kwallon kafar Najeriya, NFF," a cewarsa sanarwar.

Hukumar ta EFCC ta kara da cewa binciken da ta gudanar sun nuna cewa mutumin da ake zargi ya yi amfani da kamfanoninsa biyu wajen karkatar da kudaden.

Ta ce za a gurfanar da Muhammad Audu a gaban kuliya da zarar an kammala bincike akansa.