Abokin Trump zai sha daurin wata 40 a gidan yari

Roger Stone

An yanke wa abokin Shugaba Donald Trump, Roger Stone hukuncin zaman wata 40 a gidan yari.

An samu Stone ne da laifi a watan Nuwamba bisa tuhuma bakwai da suka hada da yi wa Majalisar Dokoki karya da hana ta aikinta da kuma bata shaidu.

Shi ne mutum na shida cikin masu taimaka wa Trump da aka tuhuma da wani mugun laifi sakamakon binciken da ake yi na Robert Mueller kan zargin yarjejeniyar sirri tsakanin Rasha da yakin neman zaben Trump a zabukan 2016.

Mista Trump ya nuna alamar yana iya yafe wa abokin nasa.

Stone ya hakikance cewa tuhumar tasa da ake yi akwai siyasa a ciki.

Da take jawabi kan hukuncin, Mai Shari'a Amy Berman Jackson ta ce an samu Stone da halayyar da ba za a iya jurewa ba, da kuma yi mata barazana.

A makon da ya gabata ne, masu shigar da kara kan shari'ar suka janye bayan da Fannin Shari'a ya ce ya shirya rage yawan lokacin zaman gidan yarin da abokin shugaban kasar da suka dadae tare zai yi.