An kama wanda ya daba wa mutum wuka a masallaci a London

'Yan sanda a cikin masallaci

Asalin hoton, @MurshHabib

Bayanan hoto,

Yadda aka dabawa wani mutum wuka a masallacin Landan

An kama wani mutum da ake zargi da yunkurin aikata kisa bayan ya daba wa wani wuka a cikin masallacin da ke tsakiyar birnin Landan.

An samu mutumin da aka daba wa wukar wanda bai wuce shekaru saba'in ba a kwance jina-jina bayan jami'an agajin gaggawa suka je masallacin da ke a Park Road kusa da wajen wasa na Regent.

An tafi da wanda aka daba wa wukar asibiti inda aka tabbatar da cewa akwai sauki a tare da shi. Jami'an 'yan sandan da suka kai shi asibitin sun ce daba wukar da aka yi wa mutumin ba shi da alaka da ta'addanci.

A cikin wata sanarwa, masallacin ya ce wanda aka daba wa wukar ladani ne a masallacin, kuma an daba masa wukar ne a lokacin sallar La'asar.

Sanarwar ta ce, wadanda suka yi sallah a masallacin ne suka kai mutumin da ya daba wukar gaban 'yan sanda.

Mai ba wa masallacin shawara, Ayaz Ahmad, ya ce daba wukar za ta iya zama barazana ga masu sallah a masallacin.

Wasu hotuna da aka dauka a masallacin sun nuna wani mutum farar fata ya sanya rigar sanyi mai hula ja da wandon jins 'yan sanda sun kwantar da shi a kasan masallacin.

Yayin da wani hoton bidiyo kuma ya nuna wuka a kan dandamalin masallacin.

Asalin hoton, @MurshHabib

Bayanan hoto,

An kama wani mutum dan shekara 29 bisa zargin yunkurin kisa

Abi Watik, wanda ganau ne, ya ce mutumin da ya kai hari da wukar yana zuwa masallacin akai-akai, kuma ya daba wa ladanin wukar ne a kafada.

Mutumin sai da ya tsaya a bayan ladanin a lokacin da ake sallar sannan kuma can sai ya daba masa wuka inji ganau din.

Miqdaad Versi, daga kungiyar Musulmai da ke Birtaniya, ya ce an shaida masa cewa an kai hari masallacin, don haka wannan abin damuwa ne.

Firaministan Birtaniya Boris Johnson, ya sanya a shafinsa na twitter cewa, " Abin damuwa ne kwarai da gaske yadda aka daba wa wani wuka a masallaci".

Shi ma magajin garin birnin Landan, Sadiq Khan, ya bayyana damuwarsa a kan harin, inda ya jajantawa wadanda abin ya shafa.