Maryam Sanda ta daukaka kara kan hukuncin kisa
Bidiyon lokacin da aka yanke wa Maryam Sanda hukuncin kisa ta hanyar rataya
Maryam Sanda ta daukaka kara a babbar Kotun Daukaka Kara da ke Abuja don kalubalantar hukuncin da aka yanke mata na kisa, sakamakon samun ta da laifi da babbar kotu ta yi na kashe mijinta.
A watan Nuwamban 2017 aka zarge ta da laifin kashe mijinta mai suna Bilyaminu Bello, wanda da ne ga tsohon shugaban jam'iyyar PDP na kasa Haliru Bello.
Kafafen yada labarai a Najeriya sun ruwaito cewa Maryam ta daukaka karar ne a ranar Alhamis, mako uku bayan Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke mata hukuncin kisa kan laifin kashe mijinta.
A takardar daukaka karar da ta rubuta wa kotun kan dalilai 20, Maryam, ta bukaci Kotun Daukaka Karar ta jingine hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yanke a kanta.
Ta yi zargin cewa alkalin kotun Mai Shari'a Yusuf Halilu ya yi hukuncin bisa son rai.
A cewarta hakan ya jawo danne 'yancinta na samun adalci da kuma yanke mata hukunci bisa amfani da hujja ta zahiri.
Bidiyon lokacin da aka yi awon gaba da Maryam Sanda
Waiwaye
A lokacin da yake yanke hukuncin, alkalin ya ce an samu dukkanin wasu shaidu da suka tabbatar da cewa Maryam ce ta aikata laifin.
Ya kuma yi watsi da ikirarinta na cewa mijin nata ya fadi ne kan fasasshiyar tukunyar Shisha, abin da ya yi sanadiyyar mutuwar tasa.
Alkalin ya kuma bayyana cewa hujjojin da aka gabatar sun gamsar da kotu cewa Maryam Sanda ta caka wa mijin nata wuka ne yayin da fada ya kaure a tsakaninsu.
A lokacin da alkali ya yanke da hukuncin wadda ake tuhuma ta yi kokarin rugawa domin guduwa daga zauren kotun sai dai jami'an tsaro sun rike ta.