Amurka da Taliban za su fara tattaunawar zaman lafiya a Afghanistan

Wani sojan Afghanistan dauke da makamin roka a yankin Kandahar, Afghanistan

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ana fatan ba za a kai wani babban hari ba a tsawon lokacin

Amurka da mayakan kungiyar Taliban za su fara tsagaita wuta na kwana bakwai a Afghanistan.

Yarjejeniyar ta za ta fara aiki ne daga karfe 12 na dare a Afghanistan, na zuwa ne bayan shafe fiye da shekara daya ana tattaunawa tsakanin wakilan Taliban da na gwamnatin Amurka.

Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya ce, "Wannan mataki na da matukar muhimmanci kuma zai taka muhimmiyar rawa wurin samar da zaman lafiya."

Idan yarjejeniyar ta yi nasara, bangarorin za su sanya hannu a bangaren farko na yarjejeniyar kawo karshen rikicin na Afghanistan da aka shafe shekara 20 ana yi.

Sanarwar da wakilan Taliban suka fitar ta ce za a samar da ''yanayin tsaro da ya dace'' kafin kulla yarjejeniyar da suke fata "zai aza tubalin zaman lafiya a fadin Afghanistan da kuma janyewar dukkan dakarun wasu kasashe daga kasar".

Da yake maraba da matakin, sakatare Janar na kungiyar tsaro ta Nato Jens Stoltenberg, ya bayyana yarjejeniyar a matsayin "muhimmin gwaji a kan gaskiyar shirin Taliban na tsagaita wuta da kuma taimaka wa wanzar da zaman lafiya".

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mayakan Taliban da wasu 'yan Afghanistan a kan mota mai sulke ta Humvee mallakar sojojin gwamnati a lokacin da aka tsagaita wuta a 2018

Gwamnatin Afghanistan, da a yanzu take fama da da rikicin sakamakon zaben shugaban kasar, ba ta daga cikin bangarorin da ke tattaunawar.

Sharuddan yarjejeniyar tsagaita wutar ta mako daya sun hada dakatar kai manyan hare-hare a kan mayakan Taliban ko dakarun kasashen waje.

Sanarwar da Pompeo ya fitar ta ce, "Mun samu fahimtar juna tsakaninmu da Taliban ce ba za mu tsagaita wuta a fadin Afghanistan."

"Idan yarjejeniyar nan ta yi nasara, ana sa ran Amurka da Taliban za su je mataki na gaba a yarjejeniyar zaman lafiya. Muna sa ran ganin an sa hannu a kan yarjejeniyar a ranar 29 ga watan Fabrairu,'' a cewar sanarwar.

Amurka ta kashe biliyoyin daloli wurin yakar kungiyar Afghanistan tun daga shekarar 2001.

Shugaba Donald Trump wanda a lokacin yakin neman zabensa a 2016 ya yi alkawarin kawo karshen yakin Afghanistan, na ta kokarin ganin dakarun kasarsa sun janye daga Afghanistan.

Wakilin BBC a Afghanistan Secunder Kermani, ya ce ana ganin matakin a matsayin wata dama da ce da shugabancin Taliban ta samu na nuna karfinsa na na fada a ji tsakanin mayakan kungiyar.

Ya kara da cewa matakin tsagaita wutan zai kuma ba da damar fahimtar juna tsakanin kungiyar da 'yan siyasar Afghanistan.