'Yan Birtaniya 12 sun shiga hannu saboda yin taba sigari ta bogi

Cigarettes discovered in Spanish factory

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

An kama kwalin tana sigari 153,000 yayin samamen

Jami'an tsaro a Spaniya sun gani wata masana'antar yin taba sigari ta karkashin kasa inda kuma suka gano wasu ma'aikata 'yan kasar waje da ke cikin mawuyacin hali kafin a ceto su.

An kuma kama wasu 'yan Birtaniya su 12 da ake tuhuma da yin taba a haramtacciyar masana'antar.

Masana'antar da ke boye a karkashin wani gidan da ake kiwon dawaki a lardin Malaga na kudancin kasar na iya samar da taba sigari ta bogi 3,500 a kowace sa'a guda.

'Yan sandan Tarayyar Turai da na kasar Spaniya sun ce wannan ce masana'antar yin taba ta karkashin kasa ta farko da aka taba ganowa a fadin Tarayyar.

An dai gano wasu ma'aikata su shida 'yan asalin kasar Ukraine da Lithuania a cikin masana'antar suna cikin wani mawuyacin hali saboda rashin iskar da za su shaka.

Wannan ya faru ne bayan da injin da ke yin famfon iska ga masana'antar ya daina aiki saboda rashin isasshen man fetur.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Masana'antar na karkashin wani gidan da ake kiwon dawaki ne a lardin Malaga

Tun da farko 'yan sanda sun kama wasu mutum 12 a harabar masana'antar, amma sai suka ki sanar da 'yan sanda cewa akwai ma'aikatansu a cikin masana'antar.

Daga nan ne ma'aikatan suka rika kururuwa, suna kuma buga abubuwa domin su ja hankalin 'yan sanda wadanda suka ceto daga dakin na karkashin kasa.

Jami'am tsaro sun kwace fakitin taba sigari 153,000 da tan 17 na tabar da ba a riga an sarrafa ta ba, da kilo 20 na hashish da kuma kilo 144 na tabar wiwi.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Masana'antar na iya samar da taba sigari 3,500 a kowace sa'a guda.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

An bar ma'aikata shida suna cikin mawuyacin hali saboda rashin iska

Akwai hakkin mallaka a kan dukkan hotunan nan.