Gwamnatin Kano ta gano yawan mutanen da suka bata a jihar

Gwamna Ganduje

Asalin hoton, Tanko Yakasai

Kwamitin binciken gano yaran da suka bata da gwamnatin jihar Kano a Najeriya ta kafa ya ce ya gano adadin yawan mutanen da suka bata a jihar.

Shugaban Kwamitin mai shari'a Wada Rano ya ce kwamitinsa ya gano mutum 113 da suka tabbatar da sun bata a jihar daga 2010 zuwa 2019.

Ya ce ta hanyar iyayen da yaransu suka bata ne suka gano yawan adadinsu, kuma akwani wani gidan marayu da ake tafiyar da shi ba bisa ka'ida ba da aka gano wasu yaran da suka bata.

Ya kara da cewa daga cikin Yaran da aka gano har da wasu guda uku 'yan kabilar Igbo daga jihar Anambra a kudancin kasar.

A watan Oktoban bara gwamnatin jihar Kano ta kafa kwamitin sakamakon kurar da ta taso bayan zargin satar kananan yara daga jihar ta Kano ana safararsu don sayarwa a yankiin kudancin Najeriya.

Wannan ya faru ne bayan 'yan sanda sun kubutar da wasu yara guda 9 'yan asalin jihar Kano da aka yi safararsu zuwa Kudu.

Wannan ne kuma janyo kiraye-kirayen gudanar da bincike, kan gano sauran yaran da suka bata a jihar.

Kwamitin ya ce zai ci gaba da aikinsa kamar yadda gwamnan jihar ya yi alkawalin aiwatar da wasu shawarwari guda 40 da ya ce ya gabatarwa gwamnati.