EFCC ta kama kwamishinan Ganduje saboda 'almundahana'

Mukhtar Ishaq

Asalin hoton, Mukhtar Ishaq/Facebook

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati a Najeriya EFCC ta ce ta kama kwamishinan ayyuka na musamman na jihar Kano Mukhtar Ishaq Yakasai.

Hukumar ta ce ta kama kwamisihinan ne ranar Alhamis bisa zarginsa da almundahanar N76m mallakin karamar hukumar Birni lokacin da yake shugaban karamar hukumar.

Wata sanarwa da mai rikon mukamin jami'in yada labarai na EFCC a Kano Tony Orilade ya aike wa BBC, ta ce matakin kamen ya biyo bayan wata takardar korafi da aka rubuta mata bisa zargin karkatar da kudaden da aka ware domin gudanar da ayyukan ci gaba da gina al'umma.

To sai dai sanarwar ta EFCC ba ta bayyana sunan wanda ya kai korafin ba.

Mai korafin ya zargi Ishaq da bayar da umarnin cire Naira dubu talatin talatin daga asusun kansiloli ba tare da wani dalili ba.

Ana kuma zargin kwamishinan da mayar da wani bangare na makarantar firamare ta Kofar Nassarawa zuwa shaguna sannan ya sayar da su a kan kudi Naira miliyan 10 kan kowane shago.

An kuma ce ya yi amfani da kudaden don kashin kansa.

A cewar sanarwar, za a gurfanar da Mukhtar Ishaq a gaban kotu da zarar an kammala bincike.

Sai dai har yanzu gwamnatin Kano ba ta ce kan batun ba.