Kotu ta yi watsi da rahoton 'dakatar' da Sarki Sanusi

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II

Wata babbar kotun tarayya a Najeriya ta soke rahoton kwamitin hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano da ya nemi a gwamnatin jihar ta dakatar da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II.

Kotun ta kuma umarnci hukumar ta biya Sarkin Naira 200,000 a matsayin kudin shari'ar da ya kashe.

Babbar kotun ta yanke hukuncin ne saboda a cewarta rashin yi wa Sarkin Kano adalci a binicken da hukumar ta gudanar game zarge-zargen da ake masa na almundahana.

A rahoton farko da kwamitin ya mika wa gwamnati ranar 6 ga Yuni, 2019, ya bukaci gwamantin jihar Kano ta dakatar da Sarkin Sanusi II har sai ta kammala bincike a kan zarginsa da almundahanar naira biliyan 3.5 na masarautar.

Amma da yake yanke hukuncin watsi da rahoton, mai shari'a O. A. Egwuatu ya ce rashin sauraren bangaren sarkin da hukumar ta yi ya saba ka'idar yi wa wanda ake zargi adalci, kuma tauye wa sarkin hakki ne.

A karar da ya shigar, Sarki Sanusi II ya bukaci kotun da ta soke rahoton kwamitin da ke da alakanta shi da zamba tare da neman a dakatar da shi.

A martaninta ga hukuncin kotun, hukumar ta yaki da cin hanci da rashawa ta Kano ta bayyana wa BBC cewa ba ta yi mamakin hukuncin ba, wanda ta bayyana a matsayin gyara kayanka.

Shugaban hukumar, Muhyi Magaji ya ce: "Tun da cewa aka yi laifinmu shi ne ba mu gayyaci Mai martaba ba, har yanzu ba abin da ya nuna cewa hukuma ba za ta yi bincike ba."

''Babu wani abin da zai hana mu kara yin rahoto irin wannan bayan mun gayyaci mai martaba sarki," in ji Muhuyi.

Ya kara da cewa, ''Za mu iya gayyatar sarki ya zo ya yi mana bayani kuma idan ya yi mana bayani muna da kwararan hujjoji da yake har yanzu abubuwan da suka sa muka yi wannan rahoto na matsayin hujja ne a a wurin mu.''

Muhyi ya ce duk da cewa sun karbi hukuncin a yadda ya zo kuma za su yi abin da ya dace, duk da cewa fahimtarsu ta saba wa ta kotun.

Game da biyan tarar da kotun ta ci hukumar, Muhyi ya ce hukumar za ta dauki matakin da ya dace a nan gaba.

''Mu a bangarenmu abin da kotu ta ce shi ne ba mu gayyaci sarki ba, shi ne abin da aka ce mun yi kuskure kuma aka rushe wannan rahoton wucin gadin da muka yi.

Lauyan sarkin, Suraj Sa'ida, ya kuma bukaci kotu ta dakatar da binciken bisa zargin cewa binciken wani bi-ta-da-kulli ne da gwamnatin Abdullahi Ganduje ke yi wa basaraken saboda goyon bayan dan takarar gwamnan jam'iyyar adawa ta PDP Abba Kabir Yusuf da ya yi a babban zaben 2019.