Ladanin masallacin Landan ya yafe wa wanda ya soka masa wuka

Raafat Maglad

Asalin hoton, PA Media

Bayanan hoto,

Raafat Maglad shi ne ladanin da wani ya daba wa wuka ana cikin sallah

Mutumin da aka daba wa wuka a cikin wani masallaci a birnin Landan ya ce ya yafe wa wanda ya kai masa harin.

Raafat Maglad, mai shekara 70 da 'yan kai ya yi jinya a asibiti bayan wani mahari ya daba masa wuka a wuya ana cikin sallah a ranar Alhamis.

Bayan dawowarsa daga masallacin da ke makwabtaka da Regent's Park a ranar Juma'a, Raafat ya ce yana tausaya wa maharin kuma ba ya jin tsanar maharin a ransa.

'Yan sanda sun tsare wani matashi mai shekara 29 da suke zargi da yunkurin aikata kisan kai, bayan masallatan da ke masallacin sun katse sallarsu sun tsare maharin.

Ra'afat wanda shi ne ladanin masallacin ya shaida wa BBC cewa ya ji "kamar an buga masa bulo," a lokacin da aka daba masa wukar daga baya.

"Na ji jini na kwarara daga wuyana, daga nan sai aka garzaya da ni zuwa asibiti. Abin ya faru da sauri-sauri ne.

Da aka tambaye shi game da saurin dawowansa masallaci da ke kwaryar birnin Landan jim kadan bayan harin, Raafat ya ce halartar sallar Juma'a na da matukar muhimmanci a gareshi.

"Idan ta wuce ni, to na rasa abu mai matukaru muhimmanci. Sallar Juma'a na da matukar muhimmanci ga kowane Musulmi.

Magajin garin Landon Sadiq Khan na daga cikin wadanda suka mahalarci sallar Juma'ar, inda ya yi kira ga masallata da su lura da abubuwan da ke faruwa a kusa da su.