Kyautar Komla Dumor: BBC na neman hazikan 'yan jaridar Afirka masu tasowa

.
Bayanan hoto,

Marigayi Komla Dumor

BBC na neman 'yan jarida masu tasowa 'yan Afirka domin bayar da lambar girmamawa ta Komla Dumor kan aikin jarida karo na shida.

Ana gayyatar 'yan jarida a fadin Afirka su nemi damar shiga gasar wadda ke fatan zakulowa da kuma tallata sabbin masu basira daga Afirka.

Wanda ya yi nasara zai yi aikin wata uku a hedikwatar BBC da ke Landan, inda za yi kwas din sanin sabbin makamar aiki.

Za a rufe karbar bukatar neman damar a ranar 16 ga Maris din 2020, da karfe 11:59 na dare agogon GMT.

An fara bayar da kyautar ne domin karrama Komla Dumor dan kasar Ghana, kwararren mai gabatar da shirye-shirye a BBC, wanda ya rasu a 2014 yana da shekara 41.

Za a kaddamar da gasar bayar da kyautar ta bana ce a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu.

Za a bayar da kyautar ga mutum daya mafi kwazo wanda mazauni ne kuma ma'aikaci a Afirka, sannan yake da kwarewa a aikin jarida da gabatar da shirye-shirye da kuma iya bayar da labarin abubuwan da suka shafi nahiyar kuma yake da burin zama taruraro nan gaba a rayuwa.

Baya ga lokacin da zai shafe tare da BBC a Landan, wanda ya lashe kyautar zai samu damar yin tafiye-tafiye a Afirka domin rubuta wani labari da za a yada a fadin nahiyar.

Wadanda suka ci kyautar a baya:

  • 2015: Nancy Kacungira daga Uganda
  • 2016: Didi Akinyelure daga Najeriya
  • 2017: Amina Yuguda daga Najeriya
  • 2018: Waihiga Mwaura daga Kenya
  • 2019: Solomon Serwanjja daga Uganda
Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Wanda ya lashe kyautar a 2019 Solomon Serwanjja, ya yi wani rahoto daga birnin Nairobin kasar Kenya, a kan wasu mutane da ke fafutukar inganta lafiyar iskar da ake shaka a birnin.

"Samun wannan kyauta na da matukar muhimmanci a gare ni, ta fuskar kwarewa da kuma kaina," inji shi.

"Samun damar yin aiki tare da takwarorin Komla wurin sauya mummunar fahimtar duniya game da Afirka a mataki na duniya ta hanyar bayar da labari ta wata fuska, babban karamci ne."

Serwanjja zai halarci bikin kaddamar da gasar ta 2020 a Johannesburg, kuma zai jagoranci gabatar da shirin muhawara a cikin shirin Focus on Africa na rediyo a BBC sashen turanci. Shirin ranar zai tattauna ne a kan makomar makamashi a Afirka da kuma yadda hakan zai yi tasiri wurin kawo ci gaba a nahiyar ba tare da karuwar matsalar sauyin yanayi ba.

Bikin kaddamar da shirin ya kunshi kai ziyara ga wasu manyan jami'o'i a Afirka ta Kudu da suka hada da jami'ar North West da ke Mafikeng da jam'iar Cape Town da jami'ar Pretoria da kuma jami'ar Johannesburg.

Manufar ziyarar ita ce ankarar da 'yan jarida masu tasowa game da ayyukan Komla Dumor domin su samun kwarin gwiwar yin hankoron samun wannan kyauta a nan gaba.

Daraktan BBC World Service Group, Jamie Angus, ya ce: "Ina alfahari da dukkan 'yan jaridar da suka samu shigowa ta hanyar kyautar Komla Dumor ta BBC, saboda kowanne daga cikinsu ya ci gaba da aikin da Komla ya fara na ba wa duniyar labarun Afirka.

"Ina maraba da haduwa da wanda ya ci gasar a duk shekarar domin in ji irin fahimtarsa game da nahiyar sannan na yi musu bayanin kudurorin BBC na aminci da tsare gaskiya - wadandasuna taka muhimmiyar rawa ga dimokradiya a duniya.

Hanyar shiga gasar

  • Domin duba cancanta da kuma shiga gasar, latsa nan
  • Za kuma ku iya yada wannan labarin na shiga gasar ta shafukan sada zumunta ta hanyar amfani da mau'du'in #BBCKomlaAward.