Taskun da matan da ba sa haihuwa ke shiga a Nijar

Taskun da matan da ba sa haihuwa ke shiga a Nijar

Wani bincike da sashen BBC na Africa Eye ya yi ya nuna taskun da matan da bas a haihuwa ke shiga a Nijar.

Wasu mazan kan musguna wa matansu dalilin rashin haihuwa inda suke kara aure domin samun haihuwa.

Amma wani likita ya bayyana cewa "yakamata su ma matan su rika matsa wa mazajensu".

Wata tsohuwa wadda bata taba haihuwa ba, ta bayyana cewa ta bi bokaye da malamai da 'yan bori duk dan ta samu haihuwa amma bata samu ba.