Rufe iyakoki ya takaita hare-haren 'yan fashi - Buhari

Shugaba Buhari da shugaban Burkina Faso

Asalin hoton, Buhari Sallau

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce an samu raguwar hare-haren 'yan fashi sakamakon rufe kan iyakokin kasar.

A cikin sanarwar da mai magana da yawun shugaban ya fitar Malam Garba Shehu, Shugaba Buhari ya ce Najeriya ta rufe kan iyakokinta ne kawai saboda tsaron kasarta.

Kuma ya ce rufe kan iyakokin ya yi tasiri sosai ga bunkasa noman shinkafa inda manoma suka samu kasuwa bayan hana shigo da shinkafa daga kasashen waje.

Shugaban ya fadi haka ne lokacin da yake karbar bakuncin shugaban Burkina Faso Roch Marc Christian Kabore wanda ya kawo ziyara Najeriya don rokon Buhari ya diba batun rufe kan iyakokin.

Shugaban Burkina Faso dai shi ne shugaban kwamitin da ECOWAS ta kafa domin shawo kan batun rufe kan iyakokin.

Sanarwar ta ce Buhari ya yi kira ga kasashen da ke makwabtaka da Najeriya su kara hakuri kan batun rufe iyakokin.

Ya ce sai ya samu rahoton kwamitin hadin guiwa da aka kafa wanda ya kunshi Najeriya da Benin da Jamhuriyyar Nijar kafin yanke shawara kan batun rufe iyakokin.

Kuma shugaban ya ce zai dauki mataki da zarar ya samu rahoton kwamitin.

Rufe kan iyakoki da Najeriya ta yi ya shafi kasashen da ke makwabtaka da ita wadanda tattalin arzikinsu ke dogaro da Najeriya.