Gwamnatin Kaduna za ta daukaka kara kan sakin 'yan Shi'a

Gwamnan Kaduna

Asalin hoton, Samuel Aruwan

Gwamnatin jihar Kaduna a Najeriya ta ce za ta daukaka kara domin kalubalantar wanke 'yan shi'a mabiya Sheikh Ibrahim el-Zakzaky da wata babbar kotu ta yi a jihar.

Kwamishinar Shari'a ta jihar Kaduna, Aisha Dikko ta shaida wa BBC cewa sun yi mamakin yadda babbar kotun ta wanke 'yan kungiyar harakar Islamiyya mabiya Shi'a kimanin dari kuma ta bayar da umarnin a sake su.

Dama dai Gwamnatin Kaduna ce ke tuhumar mabiya el-Zakzaky da laifukan da suka shafi tashin hankali, kuma tun 2015 ake tsare da su bayan kama su a Zariya lokacin rikicinsu da sojoji wanda ya yi sanadiyyar mutuwar daruruwan 'yan kungiyar ta IMN mabiya Sheikh Ibrahim el-Zakzaky.

Tuni dai kungiyar IMN ta el-Zakzaky ta bayyana hukuncin kotun a matsayin nasara da tabbatar gaskiya da adalci, wanda kuma suke fatan zai zama sanadin sakin jagoransu.

Kwamishinar shari'a ta Kaduna ta ce hujjoji da yawa suka gabatar inda suka kawo shaidu 36 da suka hada da manyan sojoji har da wadanda aka yanka da wuka.

Sannan sun gabatar da abubuwan shaida 105 da suka kunshi bindigogi da makamai da dama. "Mun yi mamakin da kotun ta ce ba ta yarda da duk shaidun da muka gabatar ba."

"Za mu daukaka kara, kuma har mun riga mun rubuta takarda inda lauyoyinmu tuni har sun karbi hukuncin kotun da ta wanke 'yan shi'ar," in ji ta.

Har yanzu shugaban kungiyar, Sheikh El-Zakzaky da mai dakinsa na a tsare a hannun hukumomin tsaron kasar, duk da umarnin sakinsu da kotuna daban-daban suka yi.