'Ba za mu fasa binciken Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ba'

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II

Asalin hoton, Instagram/sarkinkano_sunusi_fans_

Bayanan hoto,

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano da ke Najeriya ta ce za ta ci gaba da bincike kan Sarki Muhammadu Sanusi II duk da hukucin da wata kotun tarayya ta yi wanda ya soke rahotonta da ya nemi gwamnatin jihar ta dakatar da Sarkin.

Kotun, wacce ta yi yanke hukuncin ranar Juma'a, ta kuma umarnci hukumar ta biya Sarkin Naira 200,000 a matsayin kudin shari'ar da ya kashe.

Babbar kotun ta yanke hukuncin ne saboda a cewarta rashin yi wa Sarkin Kano adalci a binciken da hukumar ta gudanar game zarge-zargen da ake masa na almundahana.

A rahoton farko da kwamitin ya mika wa gwamnati ranar 6 ga Yuni, 2019, ya bukaci gwamnatin jihar Kano ta dakatar da Sarki Sanusi II har sai ta kammala bincike a kan zarginsa da almundahanar naira biliyan 3.5 na masarautar.

Amma da yake yanke hukuncin watsi da rahoton, mai shari'a O. A. Egwuatu ya ce rashin sauraren bangaren sarkin da hukumar ta yi ya saba ka'idar yi wa wanda ake zargi adalci, kuma tauye wa sarkin hakki ne.

Sai dai a tattaunawarsa da BBC, Shugaban hukumar, Muhyi Magaji Rimingado ya ce hukuncin kotun ba zai hana su kammala bincike da kuma fitar da rahoton karshe kan Sarki Sanusi II ba.

Ga cikakkiyar tattaunawar da ya yi da Ibrahim Isa:

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Muhiy: Mu a bangarenmu yadda muka kalli abin shi ne bamu gayyaci mai martaba sarki ba, kuma aka rushe rahoton kwarya-kwarya da muka yi.

To kar ka manta mu rahoton wucin-gadi muka ce mun yi, saboda haka rahoton wucin-gadi yana jiran rahoto na gaba, wanda zai zama rahoto na karshe. Mu yanzu a fahimtarmu wannan kamar wani gyara-kayanka ne, ko hannunka-mai-sanda aka yi mana kuma abin da ya kamata mu yi, za mu yi.

Ibrahim Isa: Wannan ya nuna za ku biya diyya ke nan?

Muhyi: Za mu yi abin da ya kamata, abin da ya kamata kuma wannan abu ne wanda ita hukumar za ta dauki mataki wanda kuma yanzu ba zan iya fitowa karara in ce ga abin da hukumar za mu yi ba. Amma tun da cewa aka yi mu laifinmu shi ne bamu gayyaci mai martaba ba, har yanzu ba a hana cewar hukumar ba za ta yi bincike ba. Babu wani dalili da zai hana mu kara yin rahoto irin wannan bayan mun gayyaci mai martaba Sarki.

Za mu iya gayyatar mai martaba Sarki ya zo ya yi mana bayani. Wannan ba zai hana idan muka gayyaci mai martaba Sarki ya zo ya yi mana bayani, mu kuma komawa mu ba gwamnati rahoton idan shi muka ga ya dace; idan kuma mataki ne na kotu babu abin da zai gagara.

Ibrahim Isa: Kana nufin za ku ci gaba da binciken Sarki, ba kwa gudun ku fuskanci fushin kotu tun da ta soke wannan al'amari?

Muhyi: A'a, ka fa fahimta abin da kotu ta yi; kotu ba soke bincikenmu ta yi ba. Kotu cewa ta yi ba a ji bahasi daga gare shi [Sarki] ba, duk da mun kawo hujjoji da yawa wadanda suka nuna an yi hakan. Misali, mu gwamnati muka bai wa shawara. Kuma kamar yadda muka fada a cikin hujjojin da muka gabawarta kotu, mun ce mu ba kotu ba ne ballantana a ce za mu bai wa mutum fair hearing [bahasi]. Mu hukuma ce mai bincike, kuma bincike sai aka ce an saka maka kudi a banki kuma ta tabbata cewa bankinka ne, ba laifi ba ne bisa tanajin doke sashe na 18 da ya kafa hukumarmu mu rubuta wa hukumar da abin da ya shafe mu ce ga abin da muka gani. Ku ku je ku dauki mataki kala kaza a kan wane. Su kuma suna da 'yancin daukar mataki a kan wanda muke magana a kai. Saboda haka mu abin da muke gani a yanzu, tun da kotu ce da kanta ta ce hujjar da suka kafe a kanta ke nan don bamu gayyaci mai martaba ba, ina ganin wani karfi hukumar ta sake samu ba.