Mutumin da ya soka wa ladanin masallacin London wuka zai gurfana a kotu

'Yan sanda a cikin masallacin Landan

Asalin hoton, @MurshHabib

Bayanan hoto,

An kira 'yan sanda zuwa babban masallacin birnin Landan da ke kusa da Regent's Park

A ranar Asabar ne za a gurfanar da mutumin da ake zargi da kai hari a lokacin da ake salla a babban masallacin birnin Landan.

Hukumomin Birtaniya na tuhumar Daniel Horton da laifin soka wa ladanin masallacin, Raafat Maglad wuka ana cikin sallah.

Wukar da Daniel ya daba wa Raafat, mai fiye da 70 a duniya, ana cikin sallar La'asar ta yi wa ladanin rauni a wuya.

Ana zargin Daniel da yi wa ladanin lahani da mallakar makami, inda za a gurfanar da shi a gaban kotun majistare da ke Westminster.

Raafat Maglad ya yi jinya a asibiti bayan daba masa wukar da maharin ya yi a ranar Alhamis.

Bayan dawowarsa masallacin a ranar Juma'a, Raafat ya ce ya tausaya wa maharin kuma ya ce bai tsani mutumin ba.

Asalin hoton, PA Media

Bayanan hoto,

Raafat Maglad shi ne ladanin masallacin wanda maharin ya soka wa wuka

Da aka tambaye shi game da saurin dawowarsa masallacin washegarin ranar harin, Raafat ya ce halartar sallar Juma'a na da matukar muhimmanci a gare shi.

"Idan ta wuce ni, na yi babbar asara. Sallar Juma'a na da matukar muhimmanci ga kowane Musulmi," in ji shi.

Magajin birnin London, Sadiq Khan, na daga cikin wadanda suka mahalarci sallar Juma'ar, inda ya bukaci masallata da su lura da abubuwan da ke faruwa a kusa da su.