Man United ta gayyaci wani yaron da ya rubuta wa Klopp wasika

Daragh Curley and Jurgen Klopp

Asalin hoton, Getty Images/Gordon Curley

Bayanan hoto,

Daragh Curley wrote the letter to Jurgen Klopp as part of a school project

A karon farko wani yaro dan shekara 10 zai ziyarci Old Trafford bayan ''yunkurinsa na ganin Liverpool ba ta yi nasara a gasar Premier ba''.

Daragh Curley ya aike wa kocin Liverpool Jurgen Klopp wasika, yana bukatar Liverpool ta yi rashin nasara a wasanninta masu zuwa domin kar kungiyar ta lashe gasar.

Yaron ya yi mamakin samun amsar sakonsa daga kocin na Liverpool. A nata bangaren, Manchester United ta ce tana alfahari da magoya baya irin Daragh.

''Wannan kyakkyawan labari ne. Old Trafford zai kasance cikin farin ciki,'' a cewar Daragh, bayan samun labarin takardar gayyatar.

"Abokai na za su so su samu wannan damar."

A cikin wasikarsa ga Klopp Daragh ya bayyana mai tsaron gida David de Gea da dan wasan tsakiya Bruno Fernandes a matsayin 'yan wasan da suka fi burge shi.

Ya kuma ce: "Liverpool na cin wasanni da yawa.

"Idan kuka ci wasa tara masu zuwa za ku yi zarra a gasar Premier. Kuma hakan na damu na a matsayina na magoyin bayan United.

"Saboda haka nan gaba idan Liverpool za su yi wasa, ina rokon kar a bari su yi nasara."

Asalin hoton, Gordon Curley

Bayanan hoto,

Daragh ya samu wasikar ne a farkon wannan makon

A amsar da Klopp ya rubuta, ya yaba wa yadda Daragh ke son wasannin kwallon kafa, amma ya ce Liverpool ba za ta yi asarar maki saboda bukatar tasa ba.

Liverpool na shirin cin gasar Premier, kuma har yanzu ba a yi nasara a kansu ba a kakar bana.

Wasikar Daragh ga Klopp ta ja hankalin shugabannin United, har suka gayyaci yaron da iyalensa zuwa Old Trafford.

Kakakin United ya ce hakan wani sabon salo ne na kawo wa Liverpool cikas a gasar Premier.

"Muna matukar alfahari da magoya baya kamar Daragh," inji shi.