Abokan gaba sun kafa gwamnatin hadaka a Sudan ta Kudu

Riek Machar (dama) da shugaba Salva Kiir suna yi wa 'yan jarida bayani a Juba

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Riek Machar (dama) da shugaba Salva Kiir suna yi wa 'yan jarida bayani a Juba

An rantsar da tsohon jagoran 'yan tawayen Sudan ta Kudu Rieck a matsayin mataimakin shugaban kasar Sudan ta Kudu a wani mataki na aiwatar da yarjeniyar kawo karshen yakin basasar shekara shida a kasar.

Shugaba Salva Kiir ya halarci bikin rantsar da Riek Machar a birnin Juba kuma shugabannin biyu sun dade suna zaman doya da manja tsakaninsu.

Ana fata kafa gwamantin hadin gwiwar zai kawo karshen yakin basasar da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 400,000 baya ga miliyoyi da suka yi gudun hijira a tsawon shekara shida a Sudan ta Kudu.

Bikin rantsarwar ta yau na zuwa ne gab da cikar wa'adin da aka ba shugabannin na cimma yarjejeniyar zaman lafiya. Yarjejeniyoyin da bangarorin suka kulla a baya sun sha watsewa

"Ina rantsuwa cewa zan tsare gaskiya tare da yin biyayya ga Jamhuriyar Sudan ta Kudu," Inji Machar a lokacin karbar rantsuwar fara aiki.

Daga nan sai ya rungume shugaba Kiir sannan suka yi musafaha, a taron wanda shugaban gwamantin Sudan Janar Abdel Fattah al-Burhan ya halarta.

A karkashin yarjejeniyar, an rushe majalisar ministocin kasar domin samar da gurabe ga 'yan adawa a majalisar.

Rahotanni daga kasar na cewa akwai sauran batutuwa da ba a cimma matsaya a kansu ba, ciki har da batun rabon iko da yadda za a shigar da mayakan 'yan tawayen cikin rundunar sojin kasar.

Duk da haka, bangarorin biyu sun amince da kafa gwamantin hadakar sannan daga baya su shawo kan sauran batutuwan.

An cimma yarjejeniyar ne 'yan sa'o'i kafin Majalisar Dinkin Duniyar ta fitar da rahoton da ke zargin bangarorin da jefa fararen hula cikin halin ha'ula'i da gangan domin neman mulki.

Muhimmancin yarjejeniyar

Shugaba Kiir ya bayyana cewa yana fata gwamantin ta shekara uku za ta bayar da dama ga 'yan gudun hijira a ciki da wajen kasar su koma muhallansu.

Kazalika yana fata matakin zai kawo sauki ga wanda rikicin ya jefa cikin yunwa da wahalhalu iri-iri.

Idan yarjejeniyar ta tore, to za ta bude wani sabon shafi a tarihin kasar.