Kun san abubuwan da suka faru a Najeriya a makon nan?

  • Mustapha Musa Kaita
  • Multimedia Journalist

Tun daga ranar Lahadi, 16 ga watan Fabrairun 2020 zuwa ranar Asabar, abubuwa da dama muhimmai sun faru a Najeriya kuma sun ja hankulan 'yan kasar, sai dai mun tsakuro muku kadan daga cikin muhimman abubuwan.

Abu na farko da za a iya cewa ya fi jan hankalin 'yan kasar shi ne batun Barakar da ta kunno kai a fadar shugaban Najeriya. Duba kasa domin karanta wannan labarin a takaice da ma wasu muhimmai.

'Baraka ta kunno kai a fadar Shugaba Buhari kan tsaro'

A farkon wannan makon ne dai za a iya cewa aka samu wata baraka a fadar shugaban Najeriya, bayan mai bai wa shugaban kasar shawara a kan harkokin tsaro, Babagana Monguno, ya zargi shugaban ma`aikata a fadar, Abba Kyari da yin shisshigi a cikin al`amuran da suka shafi tsaro.

Manjo-Janar Monguno mai ritaya ya ce katsalandan din da Abba Kyari ke yi a aikinsa ya takaita nasarorin da ake samu a kokarin inganta tsaro a Najeriya.

Babu dai wani martani daga bangaren shugaban ma'aikatan.

Manjo-Janar Monguno ya yi wannan zargin ne a cikin wata wasikar da ya aike wa hafsoshin tsaron kasar tun a watan Disambar 2019.

Yadda 'yan bindiga suka kashe ma'aikaciyar Aso Rock

Asalin hoton, @Nigeriapresidency

Daga batun baraka a fadar shugaban kasar sai kuma batun alhini kuma shi ma batun yana da alaka da tsaro inda a ranar Litinin ne aka samu labarin kisan da wasu da ake zargi 'yan bindiga ne suka yi wa Ms Laetitia Naankang Dagan a gidanta da ke Abuja wadda ma'aikaciya ce a fadar shugaban kasar Najeriya.

Fadar shugaban Najeriyar ta bayyana alhininta kan kisan da aka yi wa Ms Dagan, kuma kafin mutuwarta, mataimakiyar darakta ce a bangaren mulki da ke fadar.

A sanarwar, babban sakatare a Fadar Shugaban Najeriyar da ke Abuja, Jalal Arabi ya bayyana kisan da aka yi wa Ms Leticia a matsayin babban rashi ga iyalanta har ma ga daukacin ma'aikatan Fadar Shugaban Kasa.

Arabi ya kuma bayyana karfin gwuiwa cewa 'yan sanda za su gano wadanda ke da alhakin kisan Ms Dagan, kuma doka za ta yi halinta a kansu.

'Sojoji sun kona gidaje 150 a Barikin Ladi'

Asalin hoton, Getty Images

Har yanzu dai muna kan batun tsaron inda a ranar Laraba inda ba a manta ba, mun wallafa labari da ke cewa an kona gidaje da dama a samemen da ake zargin sojin Najeriya sun kai wa wata rugar Fulani a yankin Barikin Ladi.

Mazauna yankin sun tabbatar wa BBC cewa lamarin ya faru ne a safiyar Talata, kuma sun shaida cewa da alama lamarin ramuwar gayya ce sojojin suka yi domin tun asali matasa a yankin sun kai wa sojojin hari har suka kashe biyu daga cikinsu a ranar Lahadi.

Alhaji Shuaibu Bayere, shi ne shugaban kungiyar Miyetti Allah na yankin Barikin Ladi ya bayyana cewa sojojin sun kona gidaje kusan "150" har da gidansa a ciki.

BBC ta nemi jin ta bakin kakakin rundunar tsaro ta hadin gwiwa da aka dora wa alhakin tabbatar da tsaro a jihar ta Filato, sai dai bai yi wani karin bayani dangane da wannan lamarin ba.

Taron sake fasalin iyali a Musulunci a Najeriya

Asalin hoton, Buhari Sallau

A ranar Alhamis ne aka gudanar da taron sake fasalin iyali a Musulunci a Najeriya wanda aka shirya karkashin jagorancin Majalisar Koli ta addinin Musulunci da hadin gwiwar Gidauniyar Aisha Buhari ta Future Assured.

Daga cikin mahalarta taron akwai Shugaba Buhari da matarsa Aisha Buhari da shugaban majalisar dattijai Ahmad Lawal.

Taken taron dai shi "Sake Fasalin Zamantakewar Aure Domin Cigaban Najeriya,"

Yayin wannan taro, mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya yi kira ga gwamnonin jihohin Najeriya da su kirkiro da wata doka wacce za ta rage yawan mace-macen aure, da kuma kawo karshen fitintunun aure a tsakanin 'yan kasar.

Domin ganin wasu daga cikin hotunan wannan taron, ku latsa nan.

Ighalo ya kafa tarihi a Manchester United

Asalin hoton, Getty Images

A bangaren wasanni kuma a ranar Litnin, 17 ga watan Fabrairun 2020 ne dan wasan gaban Najeriya Odion Ighalo ya kafa tarihi a matsayin dan wasa na farko da ya buga wa kungiyar Manchester United wasa.

Dan wasan dai ya shiga wasansa na farko da aka kara a ranar Litnin tsakanin United din da Chelsea inda United ta ci Chelsea 2-0.

Duk da cewa minti biyu zuwa uku ya buga, wannan bai hana cewa Ighalo ya cimma burinsa na zama dan wasan Najeriya na farko da ya buga wa Manchester United wasa ba.

Wannan tarihi ya ja hankalin masana kwallon kafa la'akari da cewa United babban kulob ne a duniya, haka ma Najeriya na daya daga cikin kasashen da kungiyar ke da dimbin magoya baya a duniya.