Mene ne alfanun hukumar tubabbun 'yan Boko Haram ga Najeriya?

.

Asalin hoton, AFP

A ranar Alhamis ne dai aka gabatar da wani kudurin doka gaban majalisar dattawan Najeriya wanda zai bada dama domin sake shigar da tubabbun mayakan kungiyar Boko Haram cikin al'umma.

Tuni dai aka yi wa kudurin dokar karatu na farko a zauren majalisar kuma tsohon gwamnan jihar Yobe, Ibrahim Geidam ne ya gabatar da kudurin dokar.

Kudurin dokar na so a kafa hukumar da za a dora wa alhakin ilimantar da kuma sake shigar da tubabbun mayakan Boko Haram cikin al'umma.

Sai dai wasu 'yan kasar na nuna damuwa kan yadda ake bai wa tubabbun 'yan boko haram din muhimmanci, yayin da mutanen da suka raba da muhallansu ke cikin kuncin rayuwa.

Me kudirin dokar ke nufi?

Idan majalisar kasar ta amince da wannan kudirin ya zama doka, za a kafa wata hukuma da a karkashinta tubabbun mayakan Boko Haram din za su samu horo na musamman da kuma damar koyon sana'o'in hannu kamar aikin kapinta da dinki da dai sauransu.

Ana ganin cewa ta haka ne wadanda suka tuba daga ayyukan kungiyar za a samu gyara tunaninsu domin su koma rayuwa kamar irin ta kowa.

Mene ne amfanin kudirin dokar ga Najeriya?

  • Taimaka wa tubabbun 'yan kungiyar Boko Haram wajen amfanar kasa ta hanyar ba su dama
  • Taimaka wa gwamnati wajen samun bayanan sirri kan yadda kungiyar ke gudanar da ayyukanta
  • Bayar da damar sasanci da kara gina kasa da hadin kai
  • Wadanda ba su tuba ba kan iya tuba saboda wannan shiri na gwamnati
  • Kafa hukumar zai tamaka wa gwamnatin kasar shawo kan matsalolin tsaro da suka addabe ta.

'Wannan yunkurin zai kawo matsala ga tsaron Najeriya'

Tsohon darakta a hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya Mike Ejiofor ya bayyana cewa wannan yunkurin da kasar ke niyyar yi na kafa wannan hukuma zai kara jefa kasar ne cikin halin rashin tsaro.

Ya bayyana cewa tunanin yin afuwa ko kuma gyara tunanin wadanda suka kashe 'yan Najeriya haka kurum bai taso ba, ya ce a kowace rana 'yan Najeriyar na mutuwa sakamakon hare-haren 'yan Boko Haram.

Tuni dama 'yan kasar a shafukan sada zumunta suka fara caccaka da sukar wannan kudirin inda akasarinsu ke ganin yin hakan tamkar mayar da hannun agogo baya ne.