Za a kama mawakiya a Saudiyya

Asayel Slay

Asalin hoton, Asayel Slay

Hukumomi a Saudiyya sun yi kira da a kama wata mawakiya da ta wake matan garin Makkah a wani bidiyo ta ta saki.

Mawakiyar mai suna Asayel Slay ta wake matan garin Makkah a wani bidiyo da ta saki a shafin Youtube inda ta kwarzanta matan kasar tare da kiransu ''jajirtattu kuma kyawawa''.

Masu amfani da shafukan sada zumunta a kasar sun nuna bacin ransu karara dangane da wannan waka inda suka yi kira ga hukumomi da su damke ta.

Tun a makon da ya gabata ne dai matashiyar mawakiyar ta wallafa bidiyon a shafin Youtube.

Miliyoyin musulmi ne dai ke zuwa kasar Saudiyya domin gudanar da aikin Hajji a duk shekara.

Tun bayan da aka fara ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta kan wannan lamari, tuni aka dakatar da shafin mawakiyar na Youtube kuma aka cire bidiyon.

A ranar Alhamis ne dai gwamnan garin Makkah Khaled al-Faisal ya bayar da umarnin kama wadanda ke da hannu a sakin wannan bidiyon inda ya wallafa a shafinsa na Twitter da cewa ''hakan cin fuska ne ga al'adun Makkah''.

Tun a 2018 dai ne yariman Saudiyya mai jiran gado Mohammed bin Salman ya fara kawo sauye-sauye na tsarin kasar.

Ko a kwanakin baya sai da kasar ta bada ta sanarwar bayar da Visa ga masu yawon bude ido, haka kuma ta bada dama ga mata da maza 'yan kasashen waje da su kama dakin otal guda ba tare da an bukaci su bada shaidar alakar da ke tsakaninsu ba.

Haka zalika kasar ta kawo sauye-sauye ta bangaren nishadi da suka hada da bude gidajen sinima tare da hada casu ga manyan mawaka da shirya damben zamani na maza da mata da kuma bai wa mata izinin tukin mota.