Ana jiran sakamakon zabe a Togo

Zaben Togo

Asalin hoton, Getty Images

Yau ce rana ta farko da aka soma dakon samun sakamakon zaben shugaban kasa a Togo, bayan da aka gudanar da zaben ranar Asabar a fadin kasar.

Shugaba mai ci Faure Gnassingbe ya fuskanci abokan hamayya shidda cikin har da babban abokin hamayyarsa na dogon lokaci kuma shugaban bangaren adawa na kasar Jean-Pierre Fabre.

Wannan dai shi ne karon farko a tarihin zaben kasar da 'yan Togo da ke kasashen waje suka samu damar kada kuri'unsu, amma duk da haka rahotanni na cewa mutane dari uku ne kawai suka samu damar yin rejista a kasashen wajen.

Shugaba Gnassingbe na jam'iyya mai mulki ta Union pour la Repblique na meman wa'adi na hudu ne a wannan karo.

'Yan gidansu kuma sun shafe sama da rabin karni suna mulkin kasar.

Wannan ne karo na uku da tsohon dan jarida kuma mai fafutakar kare hakin dan Adam Jean-Pierre Fabre na jama'iyar adawa ta Alliance National pour le Changement ke tsayawa takarar shugabancin kasar.

A shekara ta 2010 da ta 2015 shi ne ya zo na biyu da yawan jama'a a zaben.

Cikin sauran 'yan takarar biyar har da tsohon firayim ministan kasar Gabriel Messan Agbeyome Kodjo, da ke wakiltar hadakar yan adawa da kuma kungiyoyin fararen hula masu rajin kare hakin dan Adam.

Ana hasashen samun sakamakon wucin gadi a cikin kwanaki shida masu zuwa.