An yi kutse a wayar ministar leken asiri a Afirka ta Kudu

Ministar AFirka Ta Kudu

Asalin hoton, Getty Images

An yi kutse a wayoyin Ministar Leken Asiri a Afirka Ta Kudu Ayanda Dlodlo da mataimakinta Zizi Kodwa.

Masu bincike na duba ta yadda aka yi kutse a wayoyinsu da kuma wayoyin wasu jami'an leken asiri, a cewar ma'aikatar tsaron.

Sai dai ba bu masaniya kan wanda yake da hannu a lamarin ko kuma an yi kutse kan mahimman bayanai, in ji ma'aikatar.

Mai magana da yawun Dlodlo ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cew an gano kutsen lokacin da mutane da dama suka ga sakon karta-kwana daga Kodwa.

Lamarin dai na zuwa ne 'yan makonni bayan an kutsa cikin hedkwatar hukumar tsaron kasar da ke Pretoria babban birnin kasar.

Barayi sun shiga wajen ajiyar mahimman bayanai a ofishin tare da tafiya da wasu takardu da kudade da ba a san yawansu ba kamar yadda aka wallafa a shafin IOL da ke intanet.