Liverpool da Man Utd na zawarcin Bellingham, Milan na son sayo Aubameyang

Birmingham's Jude Bellingham

Asalin hoton, Getty Images

Liverpool ta bi sahun kungiyoyin da ke fafafawa domin sayen dan wasan Birmingham mai shekara 16, Jude Bellingham, wanda za a sayar a kan £30m kuma ake rade radin zai koma Manchester United. (Star on Sunday)

Inter Milan na shiri domin sayo dan wasan Arsenal Pierre-Emerick Aubameyang, mai shekara 30, a bazara, inda aka ce sun ware £92m domin dauko dan kasar ta Gabon. (Express)

Manchester City za ta yi "dukkan abin da ya kamata" wajen ganin an janye haramcin da aka yi mata na buga gasar Turai tsawon shekara biyu, wanda zai iya sanya wa a gurfanar da Liverpool a kotu a kan zargin yin kutse cikin shafin intanet na ajiye bayanan kananan 'yan wasan City. (Tuttosport via Mirror)

Real Madrid za ta kalubalanci Manchester City wajen sayo dan wasan Napoli dan kasar Spain mai shekara 23, Fabian Ruiz, wanda za a sayar a kan £80m. . (Express)

Leicester za ta sake taya dan wasan Celtic mai shekara 26, Callum McGregor, wanda kudin sayensa ya kai £25m. (Sun)

A shirye Manchester United take ta sayo dan wasan Wolves da Portugal Diogo Jota, mai shekara 23, a kan £50m a bazara mai zuwa. (Express)

Sheffield United za ta ware £20m domin sayo dan wasan Leeds dan kasar Ingila Kalvin Phillips, mai shekara 23. (Sun)

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Dan wasan RB Leipzig dan kasar Jamus Timo Werner, mai shekara23, wanda ake hasashen zai koma Liverpool, ya bayyana Jurgen Klopp a matsayin koci mafi kwarewa a duniya. (Mail)

Dan wasan tsakiya na Aston Villa kuma kyaftin Jack Grealish, mai shekara 24, ya dage cewa yana shakkar rade radin da ake yi cewa zai koma Manchester United ko Liverpool. (Express and Star)

Kocin Jiangsu Suning Cosmin Olaroiu ya ce a bara sun cimma kashi 90 cikin 100 na yarjejeniyar da suke kullawa domin dan wasan Real Madrid Gareth Bale, mai shekara 30, ya koma China a bazara mai zuwa a matsayin aro, amma yarjejeniyar ta wargaje bayan Real ta bukaci kudi a kansa (Goal.com)

Dan wasan Manchester City dan kasar Ingila Phil Foden, mai shekara 19, ya ce yana farin cikin ci gaba da zama a kungiyar maimakon ya tafi wata kungiyar a matsayin aro. (Manchester Evening News)

Chelsea na sha'awar sayen dan wasan Inter Milan Mauro Icardi, wanda yanzu haka Paris St-Germain ta yi aronsa kuma mai yiwuwa ta sayi dan wasan mai shekara 27 a lokacin musayar 'yan kwallo a bazara. (Sport Witness)

Jose Mourinho ya amince cewa zai yi "matukar wahala" Tottenham ta kammala gasar bana a cikin 'yan hudun farko a saman teburin gasar Firimiya (Talksport)

Dan wasan Manchester United da Serbia Nemanja Matic, mai shekara 31, yana son ci gaba da zama a Old Trafford ko da kuwa kwantaraginsa ta kare a bazara. (Mirror)