Hotunan abubuwan da suka faru a Kannywood makon jiya

'Yar da aka haifa wa Abba Maishadda

Asalin hoton, Intagram/realabmaishadda

Bayanan hoto,

Furodusa Abubakar Bashir Maishadda ya samu karuwa ta haihuwa. Matarsa ta haifi zankadediyar budurwa wadda ya wallafa hotonta a shafinsa a ranar Asabar. 'Yan uwa da masoya da abokan sana'a na ta addu'o'in taya murna

Yakubu Usman Mpeg

Asalin hoton, @realalinuhu

Bayanan hoto,

Editan Kannywood Yakubu Usman Mpeg, ya yi bikin zagayowar ranar haihuwarsa a ranar Asabar 22 ga watan Fabrairu. Jaruman masana'anta da masoyansa sun yi ta aika masa sakonnin taya murna

Asalin hoton, @officialkannywood

Bayanan hoto,

Dambarwa ta kunno kai bayan Yusuf Haruna (Baban Chinedu) ya zargi shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano Isma'il Na'Abba Afakallahu, da karkatar da naira miliyan biyar da gwamantin jihar Kano ta bayar a matsayin gudummuwa a lokacin bikin diyar marigayi Rabilu Musa Ibro

Asalin hoton, @nura_m_inuwa

Bayanan hoto,

Ko dai an yi wa Nura M Inuwa nadin sarauta ne? Wacce saurauta aka ba sh? Irin wannan nadi haka!

Asalin hoton, @officialkannywood

Bayanan hoto,

Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta ce dole tauraron Kannywood Adam Zango ya bi dokokinta idan yana so ya je jihar domin gudanar da harkokin fim. Hakan na zuwa ne bayan bidiyon da Rahama Sadau ta wallafa na Zango yana cewa zai je Kano domin kallon fim din 'Mati A Zazzau'. A nan, Adam Zango ne da shugaban hukumar, Isma'ila Na'abba Afakallah lokacin suna dasawa.

Asalin hoton, @namenj

Bayanan hoto,

Namenj ya fitar fitar da hotonsa a lokacin daukar wata waka da ya yi cikin harshen turanci.

Asalin hoton, @mustapha_nabraska

Bayanan hoto,

Allah Ya raya 'yan mata, Ya kara wa mai jego lafiya! Jarumi Mustapha Nabraska ya samu karuwar 'ya mace a ranar Asabar 22 Fabrairu, 2020.

Bayanan hoto,

Tauraruwar Kannywood, Aisha Dankano ta cika shekaru hudu da rasuwa. Allah Ya garfarta mata, mu ma idan ta mu ta zo Allah Ya sa mu yi kyakkyawan karshe