Mutanen Borno sun soma azumi da addu'o'i kan Boko Haram

Babagana Zulum

Asalin hoton, Twitter/@govborno

Ranar Litinin al'ummar jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya suka tashi da azumi da addu'o'i da zummar neman saukin masifar da mayakan kungiyar Boko Haram suka jefa su a ciki.

Mayakan na Boko Haram sun kwashe fiye da shekara goma suna kai hare-hare a arewacin Najeriya, musamman a jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa.

Hare-haren sun yi sanadin mutuwar dubban mutane da kana suka raba miliyoyin jama'a da gidajensu.

Malam Abdulmumin Yunus, wani malamin addinin Musulunci a Maiduguri, ya shaida wa BBC muhimmancin yin azumin da addu'o'i.

"Da ma ya tabbata a cikin addinin Musulunci cewa duk lokacin da wata matsala ta taso, mutane suna iya tawassuli da ayyuka na alheri da nufin Allah ya dauke wannan masifa da ake ciki.

Dangane da azumin da mai girma ya ce a yi, abu ne da lallai mutane sun kabe shi kwarai da gaske. Akwai wadanda ba Musulmi ba ne wadanda muka tattauna da su suka ce za su yi irin nasu nau'in na ibada" in ji shi.

A makon jiya ne gwamnan jihar ya bukaci a tashi da azumi da addu'o'i ranar Litinin 24 ga watan Fabrairun 2020 domin neman sauki kan Boko Haram.

Ya bayyana haka ne yayin wani jawabi na minti shida da yayi wa jama'ar jihar.

Sai dai gwamnan ya ce ba wai ranar hutu bace domin za a je aiki a ranar Litinin din.

Ya bayyana cewa wasu za su ga wannan lamarin kamar wani sabon salo, amma hakan ya zo ne sakamakon kiraye-kirayen da jama'a ke yi na yin hakan.

Asalin hoton, Getty Images

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Ya ce a matsayinsa na gwamnan jihar zai yi azumi ranar Litinin kuma ya yi kira ga kowa ya yi hakan.

Kazalika, gwamna Zulum ya yi kira ga 'yan uwa da abokan jihar da su yi azumi a ranar domin dawowa da zaman lafiya a jihar.

Gwamnan ya kara da cewa tuni Shehun Borno ya tabbatar masa cewa duka limamai na kananan hukumomi 27 da ke jihar za su yi addu'o'i da Qunuti a duka salloli biyar na ranar Litinin.

Ya kuma ce shugabannin Kiristoci a jihar sun yi masa alkawarin yin addu'o'i na musamman a coci a ranar ta Litinin.

Gwamnatin Buhari dai ta dade tana ikirarin karya lagon kungiyar Boko Haram da ta addabi yankin arewa maso gabas, amma har yanzu mayakan kungiyar na ci gaba da yi wa mutanen yankin barazana.

Ko a kwanakin baya sai da 'yan kungiyar suka kai hari a Auno da ke jihar ta Borno inda suka kashe fiye da mutane 30.

Lamarin dai ya sa wasu al'umar jihar ta Borno sun yi wa Shugaba Buhari ihu lokacin da ya je domin ya jajanta musu.

Karin labaran da za ku so ku karanta: