Dalilan kasashen Yamma na kara kulla zumunci da Afirka

Taron kolin da aka yi tsakanin China da kasashen Afirka a bara ya samu halartar akasarin shugabannin Afirka

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Taron kolin da aka yi tsakanin China da kasashen Afirka a bara ya samu halartar akasarin shugabannin Afirka

Manyan kasashen duniya na ta kara mayar da hankali wajen kara habaka karfin siyasarsu da kuma tattalin arzikinsu ga kasashen Afirka, amma me ya kawo wannan sabon yunkurin na manyan kasashen a nahiyar Afirka kuma me kasashen nahiyar ke yi dangane da haka?

Wakilin BBC Dickens Olewe ya yi nazari dangane da wannan batu.

A cikin 'yan shekarun nan, 'yan nahiyar Afirka na ganin yadda shugabannin kasashensu ke keta hazo domin amsa gayyatar da manyan kasashe ke musu domin halartar taruka a fadin duniya.

Akasarin tarukan ana cewa ana yin su ne da zummar amfanin kasashen da aka gayyata da kuma kasar da ta yi gayyatar.

A bara, kasashen Japan da Rasha sun gayyaci shugabannin kasashen Afirka; a watan da ya gabata, shugabannin Afirka 15 ne suka halarci taron zuba jari na Birtaniya da aka gudanar a Landan.

Kuma kamar yadda rahotanni ke bayyanawa, tuni aka tura irin wannan goron gayyatar ga kasashen domin halartar irin wannan taron da ake sa ran yi a Faransa, da Saudiyya da kuma Turkiyya duk a wannan shekara.

Asalin hoton, AFP

Wane buri manyan kasashen ke son cimma wa?

Haka zalika, kuri'u 54 wadanda kasashen ke da su a Majalisar Dinkin Duniya da kara habakar ayyukan masu ikirarin jihadi da habakar tattalin arziki a nahiyar ta Afirka na cikin dalilan kasashen yamma na kara kusantar Afirka.

Wata mai sharhi kan tattalin arziki a kasar Zambiya Dakta Dambisa Moyo ta bayyana cewa: ''Akwai bukatar kasashen duniya su tallafa wajen kawo karshen matsalolin Afirka idan ba haka ba nan gaba matsalolin za su shafi kasashen duniya''.

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya yarda da wannan batu inda a wata ziyara da ya kai cikin 'yan kwanakin nan Amurka ya bayyana cewa: ''Afirka na samar da barazanar tsaro da kuma samar da 'yan gudun hijirar masu dumbin yawa,'' amma duk da haka nahiyar na kawo ci gaba ta fannin zuba jari ga duniya.

Sai dai ya yi gargadi dangane da dangantakar da ta yi tsami tsakanin Amurka da China da Rasha da wasu kasashen.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Wani kamfani a Uganda kenan da ke hada wayoyin salula

Shin shugabannin Afirka na da wani shiri na musamman?

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

A 2013, shugabannin nahiyar karkashin Kungiyar Tarayyar Afirka AU, sun amince kan wani tsari wanda ke kunshe da yadda za a shawo kan matsalolin da nahiyar ke fuskanta.

An yi wa shirin lakabi da ''Agenda 2063''.

Shirin na dauke da tsare-tsare da kuma hanyoyi kan yadda za a shawo kan yakin da ke faruwa a nahiyar da kara gina ababen more rayuwa a yankin da kuma samar da damar zirga-zirga ba tare da takura ba ko barazana a nahiyar.

Wani daga cikin babban shirin da nahiyar ke da shi, shi ne na yarjejeniyar kasuwancin kai tsaye ta nahiyar, wanda shiri ne mafi girma a duniya kuma irin wannan shirin na dauke da kasashe masu yawa.

An tsara shirin ne domin kara habaka kasuwanci tsakanin kasashen nahiyar.

Sai dai masu sharhi na ganin wannan shirin na yarjejeniyar kasuwancin kai tsaye wanda ake sa ran farawa a watan Yuli ba zai kawo mafita ba, kuma akwai kalubale iri-iri a tattare da shirin musamman abubuwan da suka shafi rashin hanyoyi masu inganci na kai kayayyaki a kasashen na Afirka.

Manyan ayyuka na ''Agenda 2063

  • Shirin zai hada manyan babban biranen Afirka ta hanyar layin dogo na jirgin kasa
  • Shirin zai kara habaka kasuwanci tsakanin kasashen Afirka da kuma kara karfin tattalin arzikin Afirka a kasuwannin duniya
  • Kara habaka madatsar ruwar Inga da ke Jamhuriyyar Dimkoradiyar Congo domin samun wutar lantarki da ta kai girman 43,200 MW
  • Cire shinge ga matafiya 'yan nahiyar, da kuma damar aiki da zama ga 'yan nahiyar a kowace kasa
  • Kawo karshen duka rikice-rikice, da yakin basasa da rikicin da ya shafi jinsi da kiyayar kisan kiyashi
  • Kara habaka fannin jiragen sama na nahiyar
  • Kafa Jami'ar Afirka Ta Intanet
  • Samar da wani rumbu na bayanai na musamman na tarihin Afirka da kuma yanayin rayuwarsu

Majiya: Agenda 2063

Sai dai Kungiyar Tarayyar Afirka AU na ta gwagwarmaya wajen cimma muradun 2063 sakamakon kungiyar ba ta da karfin tankwara kasashen da ke karkashinta domin ba da muhimmanci ga shirin, kamar yadda tsohon Ministan Ayyuka a Liberiya W Gyude Moore ya bayyana.

Ya shaida cewa akasarin kasashen na Afirka na kokarin biyan basussukan da ake binsu ne ba kokarin yin wadannan ayyukan na Agenda 2063 ba.