Trump da matarsa sun ziyarci cibiyar soyayya ta duniya a Indiya

US President Donald Trump and First Lady Melania Trump pose as they visit the Taj Mahal in Agra on February 24, 2020.

Asalin hoton, Getty Images

Shugaban kasar Amurka Donald Trump da mai dakinsa Melania sun ziyarci cibiyar soyayya ta Taj Mahal da ke Indiya a ranar farko da suka isa kasar.

Wurin ya kasance waje na biyu da Mr Trump ya ziyarta a yayin ziyarar aikin da ya je Indiya.

Da farko sai da Trump ya fara isa Gujarat, wato jihar Firai Minista Narendra Modi, inda aka masa tarbar alfarma.

Daga nan ne kuma Mista Trump da matarsa suka wuce zuwa cibiyayyar soyayya ta Taj Mahal.

Namaste, Indiya

A yayin da ya isa Gujarat, Shugaba Trump ya gabatar da jawabi ga dubban mutane a babban filin wasan da ke jihar.

Mista Trump ya fara jawabin nasa ne cewa " Namaste" wato gaisuwar 'yan kasar Indiya kenan.

Trump ya ci gaba da cewa "Indiya na gurbi na musamman a zuciyarmu".

Sannan ya ci gaba da sauran jawabai ga al'ummar kasar.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An yi wa Mista Trump tarba ta musamman a Agra

Daga nan Mista Trump ya yi kokari ya fadi wasu kalmomi da Indiyanci.

Mista Trump ya karkare jawabinsa da cewa "Allah ya ja zamanin Indiya, Allah ya ja zamanin Amurka, muna matukar kaunarku sosai da sosai".

Ziyarar ta Mista Trump na zuwa ne a daidai lokacin da Mista Modi a 'yan kwanakin nan ya yi kaurin suna sakamakon wadansu matakai da gwamnatinsa ta dauka da suka janyo ce-ce-ku-ce.

A watan Disambar 2019 ne, gwamnatin kasar ta Indiya ta amince da sabuwar dokar bai wa 'yan ci-rani damar zama 'yan kasa a Indiya, dokar dai ta bai wa baki da ba Musulmi ba da suka fito daga kasashen makwabta uku na Indiya damar zama 'yan kasa.

Bayanan hoto,

Fiye da mutane dubu 100 ne suka taru a filin wasa Motera

Mista Modi dai ya shirya wa Shugaba Trump hadaddiyar liyafa.

An dai yi bukukuwa kala-kala tare da nuna al'adu da wasanni da dama domin zuwan Trump.

Cikin wuraren da Trump ya ziyarta har da Sabarmati Ashram, inda jagoran 'yancin kasar Indiya Mahatma Gandhi ya zauna.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Shugaba Trump da mai dakinsa Melania

To sai dai kuma duk da kade-kade da raye-rayen da aka yi a yayin ziyarar Trump, yarjejeniyar kasuwancin da aka jima ana jira a cimma ba a kai ga cimmata ba.

Amurka na daya daga cikin manyan abokan huldar kasuwancin India.

Duk da dangantakar siyasa da ta tsaro da ke karuwa a tsakanin kasashen biyu, akwai wasu matsaloli a dangantakar kasuwancin da ke tsakaninsu.

Mista Trump ya ce harajin da Indiya ke sanyawa a kan kayayyakin da ake shigar da su kasarta ya yi yawa, sannan ya bayyana Indiya a matsayin uwar karbar haraji.