EFCC ta sake gurfanar da Jonah Jang gaban kotu

.

Asalin hoton, @officialEFCC

Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya EFCC ta sake gurfanar da tsohon gwamnan jihar Filato Sanata Jonah David Jang da kuma Yusuf Pam wanda tsohon kashiya ne ko mai ajiya da bayar da kudi a ofishin sakataren gwamnatin jihar.

Hukumar ta gurfanar da su ne gaban Mai Shari'a C.L Dabup a kotun jihar ta Filato kan zarge-zarge 17.

Hukumar ta EFCC na zarginsu ne da almundahanar kudaden jihar da suka kai naira biliyan 30.

Tun a baya dai, an taba kai wannan karar a gaban Mai Shari'a Longji wanda kafin ya yi ritaya daga alkalanci a 31 ga watan Disambar bara, ya soke bahasin wadanda ake zargin inda suke cewa ba su aikata laifin almundahana ba musamman kan batun kudaden kanana da matsakaitan masana'antu da Babban Bankin Najeriya ya ba jihar da kuma na hukumar SUBEB da ake zargin sun karkatar.

Wadanda ake zargin dai sun ki amincewa da laifukan da ake zarginsu aikatawa, bayan haka lauyan da ke karar mutanen biyu ya bukaci kotun ta saka ranar fara shari'ar.

Lauyoyin da ke kare wadanda ake karar E.G Phajok, (SAN), da S.G Ode sun bukaci a bayar da belin wadanda suke karewa inda suka roki kotun ta tsaya kan belin da Alkali Longji ya bayar a can baya.

A karshe Mai Shari'a Dabup ta bayar da beli ga wadanda ake zargin inda ta dora kan hujjojin Alkali Longji inda ta bukaci masu tsaya musu da su cika takardu idan suna so su ci gaba da tsaya musu.

Ta bayar da kwanaki uku domin cika sharuddan belin kuma ta saka ranar fara shari'ar daga 26 zuwa 28 na Mayun 2020.

Tsofaffin gwamnonin Najeriya da aka tura gidan yari

Joshua Dariye

Jiha: Filato

Mukami: Tsohon gwamna

Hukunci: Shekaru 14 cikin gidan yari sakamakon samunsa da laifin almundahanar naira biliyan 1.6

Rana: Yunin 2018

Diepreye Alamieyeseigha (Marigayi)

Jiha: Bayelsa

Mukami: Tsohon gwamna

Hukunci: Daurin shekaru biyu a gidan yari kan laifuka shida na almundahanar kudi da suka kai biliyan 1.6

Rana: Yulin 2007

James Ibori

Jiha: Delta

Mukami: Tsohon gwamna

Hukunci: Daurin shekaru 13 a gidan yari kan laifuka 10 da suka shafi kulla makirici domin almundahana da kuma fitar da kudi ba kan ka'ida ba (dala miliyan 77)

Rana: Afrilun 2012

Jolly Nyame

Jiha: Taraba

Mukami: Tsohon gwamna

Hukunci: Shekaru 28 a gidan yari kan laifuka 41 daban-daban.

Rana: Mayun 2018